1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al´ammura sun fara daidaita a filayen saukar jiragen samar Turai

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bumk

Al´ammura sun fara daidaita, a filayen saukar jiragen samar turai, kwanaki 4, bayan yunkurin shirya ta´adanci da jami´an tsaron Britania su ka gano, a kann jirage masu zirga zirga, tsakanin Engla da Amurika.

Ya zuwa yanzu, jikirin tashin jirage, ko kuma fasa tashin su ma gaba daya, sun fara sauki, a mafi yawan filayen saukar jiragen saman nahiyar turai.

Saidai a Britania, hukumomin kulla da zirga zirga, sun bullo da wasu sabin dokoki, na hana shiga jirgi, da duk wani abu, mai kama da ruwa, banda madara shayar da yara, wada itama sai mutum ya dandana, don tabatar da cewa ba ta dauke da wata guba, da za a iya anfani da ita ,domin tarwatsa jirgi.

A kasar France, campanin Air France, ya koma tsofan aikin sa, na tada jirage 12, kulum daga filin saukar jiragen sama Charles Degaule ,na birnin Paris, zuwa filin jirgin Heathrow na Britania.

Gobe idan Allah ya kaimu, ministocin suhuri, na kasashe 25, membobin kungiyar gamaya turai, za su shirya zaman taro, a birnin London, domin mahaurori a kan matakan bai daya, na yaki da ta´danci a jiragen sama.