1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ke haifar da cutar Cancer?

Babangida Salihu JibrilDecember 8, 2009

Cutar Cancer ko Sankara dai cuta ce dake haifar da wani tsuro a jikin bil'adama wanda ke shafan ƙwayoyin halitan bil'adama

https://p.dw.com/p/KwTm
Wasu masu ɗauke da cutar Cancer a cibiyar binciken cutar Cancer a TanzaniyaHoto: A.Leuker, IAEA

Cutar Cancer ko Sankara dai cuta ce dake haifar da wani tsuro a jikin bil'adama wanda ke shafan ƙwayoyin halitan bil'adama wanda kuma ke kaiwa ga nakasan wani ko dukkan ɓangaren bil'adama kuma sauda yawa ma dai hakan kan kai ga rasa rayukan masu ɗauke da wannan cuta.

A shekara ta 2008, Hukumar lafiya ta Duniya tayi ƙiyasin cewar akwai mutane miliyan 12.4 da suka kamu da cutar. A yayin da kuma mutane miliyan 7.6 ne suka rasu a sakamakon kamuwa da cutar, wasu miliyan 25 kuma ke fama da cutar na tsawon shekaru biyar. kafin nan da shekara ta 2030 kuwa, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO tayi bayani kimanin mutane miliyan 17 ne zasu rasu sakamakon kamuwa da cutar ta Cancer, ayayinda wasu miliyan 26 kuma zasu kasance masu ɗauke da cutar.

Rahotannin sun tabbatar da cigaba da yawaitar masu kamuwa da wannan cuta a ƙasashe masu tasowa wa'yanda yanzu haka suke da masu ɗauke da cutar har kashi 60 cikin 100, lamarin da aka danganta da ƙaruwa ko cigaba da runguman hanyoyin rayuwa na yanmacin Turai, yankin da ada itace tafi sauran sassan duniya yawan masu ɗauke da masu wannan cuta.

Sai dai kuma masana harkar lafiya sun bayyana cewar kowane yanki ko nahiyar duniya akwai cutar ta Cancer da tafi ƙamari a tsakanin al'uman wannan yanki. Misali itace yadda cutar cancer ta mafitsara tayi ƙamari tsakanin maza a ƙasashe masu tasowa, inda ake samun mutane uku cikin 500 dake ɗauke da ita. A yayin da Cancer ta Mama ko mahaifa tafi ƙamari tsakanin kuma mata. Wannan lamari ne ma yasa Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta ware rana ta musanman domin faɗakar wa game da illar wannan cuta.

Cancer Diseases Hospital Zambia 1
Asibitin masu fama da cutar Cancer a ƙasar ZambiaHoto: A.Leuker, IAEA

Masana kimiyan lafiya sun tabbatar da cewar akwai cutukan Sankara ko Cancer kimanin 100 dake addabar jama'a a duniya. kuma kowane ɗaya daga cikin wa'yan nan cutukan na Cancer nada nashi alamomi, a yayinda wasu kuma suke kama da wasu. Kaɗan daga cikin alamomin cutar ta Cancer dai sun haɗa da yawan nuna laulayi da rama da kuma zazzaɓi ko rage zuwa ban ɗaki kamar yadda mutum ya saba. Sauran lamun cutar ta Cancer kamar yadda masana sukayi bayani sun haɗa yawan Tari babu ƙauƙautawa da kuma fitar da jini ko majina a lokacin wannan tari. Wannan alamu dai anfi dangantashi da sankara ta huhu.

Wasu daga cikin cutukan na Cancer ko Sankara da ake dasu dai sun haɗa data Mama da Mahaifa waɗanda sukafi ƙamari a tsakanin mata. Haka kuma akwai Cancer ta huhu datafi ƙamarai tsakanin masu shan taba Sigari, haka kuma akwai Sankara ta fatar jiki data ciki. Bayan wannan kuma akwai sankara ta jini wato Leukemia da kuma ta ƙashi. Bayan waɗannan kuma akwai Sankaran dubura bayan nan kuma akwai Sankaran ƙwaƙwalwa. To amma dai dukkannin waɗannan cutuka na Sankara masana harkokin lafiya na ganin ana iya magance kashi 1/3 ko kuma rage lahanin da zasu iya yiwa ɗan adam muddin aka gano su akan lokaci, kuma akayi anfani da magungunan da suka dace, duk kuwa da yanke ƙaunar da ake ɗorawa duk wanda ya kamu da ɗaya daga cikin wannan cuta ta Sankara.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita:Abdullahi Tanko Bala