1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun kawo karshen dambaruwar siyasa a Iraki

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1A

Kusan watanni 4 bayan zaben ´yan majalisar dokoki, yanzu an fara ganin la,amar kawo karshen dabaruwar siyasa a Iraki. Yanzu haka dai bayan FM Ibrahim al-Jaafari da ake kai ruwa rana a kansa ya sauka, kawancen jam´iyun ´yan shi´a sun amince su nada Jawad al-Maliki a mukamin sabon FM. an Sunni da kuma Kuradawa sun nuna alamun amincewa da nadin Maliki a matsayin magajin al-Jaafari. Takaddama da ake yi tsakanin Kurdawa da ´yan Sunni da kuma ´yan Shi´a dangane da mukamin FM ya janyo tarnaki ga shirin kafa gwamnati a Iraqi tun bayan zaben ´yan majalisar dokoki a cikin watan desamban bara. A yau asabar ake sa ran cewa majalisar dokokin Iraqi a birnin Bagadaza zata yi zama don duba batun raba manyan mukamai a cikin sabuwar gwamnatin da za´a kafa.