1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amura sun rincaɓe a Bangkok

May 14, 2010

Tsakiyar birnin Bangkok a ƙasar Thailand ya zama wani filin daga

https://p.dw.com/p/NOWx
Hoto: AP

Dakarun gwamnatin ƙasar Thailand sun buɗe wuta da harsasai da hayaƙi mai sa hawaye akan 'yan jajayen riguna dake zanga-zanga a yankin hada-hadar kasuwanci na birnin Bangkok, inda suka halaka aƙalla mutane goma sannan suka yiwa fiye da 100 rauni. Sojojin dai sun kutsa tsakiyar birnin ne da maraicen yau Jumma'a domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka shafe watanni biyu suna fito na fito da jami'an tsaro. Waɗanda suka shaida abin da ya faru sun ce sun ji ƙarar fashewar bama-bamai.

Masu zanga-zangar dake adawa da gwamnatin Firaminista Abhisit Vejjajiva sun cunnawa motocin 'yan sanda wuta. An toshe dukkan hanyoyin dake shiga yankin hada-hadar cinikin domin hana ƙarin masu bore shiga yankin. An dai kafa dokar ta-ɓaci a wasu birane na ƙasar ciki kuwa har da Bangkok.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi