1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alan Garcia ya lashe zaben shugaban kasar Peru

June 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuvP

Mai ra´ayin social democrat kuma tsohon shugaban Peru Alan Garcia ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar. Kamar yadda hukumar zaben kasar a birnin Lima ta nunar, Mista Garcia ya samu kashi 55 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada. A halin da ake ciki babban abokin hamayya kuma mai ra´ayin kishin kasa Ollanta Humala ya amince da kayen da ya sha. Garcia ya taba zama shugaban Peru daga shekarar 1985 zuwa 1990. To amma wa´adin mulkinsa ya kawo karshe cikin wani hali na rudamin tattali arziki da siyasa. Bayan wannan nasara da ya samu a zaben, Garcia yayi alkawarin inganta yanayin zamantakewar al´umar kasar ta Peru. Kimanin kashi 50 cikin 100 na al´umar wannan kasa dake kudancin nahiyar Amirka su mutum miliyan 27 ke fama da talauci.