1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alasane Ouattara zai halarci gun jana´izar mahafiyarsa a birnin Abidjan

December 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvIG

Madugun ´yan adawar kasar Ivory Coast Alasane Watara wanda ya yi kaura zuwa Faransa bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a shekara ta 2002, zai koma gida don halartar jana´izar mahaifiyar sa. Gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo na zargin Watara mai shekaru 63 da haihuwa kuma tsohon FM daga arewacin Ivory Coast da angiza boren da ya raba kasar gida biyu wato ´yan tawaye na iko da arewa yayin gwamnati kuma ke rike da yankin kudancin kasar. Ali Coulibaly kakakin Watara ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa Watara zai je gida don halartar jana´izar mahaifiyarsa wadda ta rasu a ranar laraba da ta gabata. Kakakin ya ce a farkon makon gobe za´a sanya ranar da Watara zai tashi zuwa Ivory Coast domin halartar jana´izar mahaifiyar ta a wadda za´a yi a birnin Abidjan a ranar alhamis mai zuwa. A cikin watan satumba tsohon shugaban kasa kuma mai adawa da shugaba Gbagbo, Henri Konan Bedie ya koma Abidjan bayan kaurar da yayi zuwa Faransa.