1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Algeriya ta koro baki yan ci-rani zuwa Nijar

Salissou Boukari
August 29, 2017

Hukumomin Algeriya sun tiso keyar wasu 'yan kasashen Nijar, Najeriya, Gambiya da ma Sudan da suka je kasar ci- rani ya zuwa jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar wandanda yawansu ya kai sama da mutun 1000.

https://p.dw.com/p/2j2PE
Niger Konvoi in Agadez
Masu zuwa ci rani daga jihar Agadez a Jamhuriyar NijarHoto: DW/A. Kriesch

Bakin haure 'yan Kasar Nijar da saura 'yan kasashen waje dubu daya da 'yan kai ne kasar Algeriya ta tiso keyar su zuwa jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar. Daga cikin su akoye 'yan kasar Nigeriya, Sudan da kuma Gambiya. Sai dai da shigowar su kasar ta Nijar hukumomin birnin Arlit da ke jihar Agadez sun karbe su da hannu biyu-biyu tare da basu kulawar da ta kamata a fannin kula da lafiya, da samar musu da abinci kafin daga bisani a fice da su ya zuwa birnin Agadez.

Bayan hukumomin na Agadez sun tantance su, suma za su dauki matakai na kai su ya zuwa garuruwan su ga wadanda suke 'yan Nijar, yayin da sauran 'yan wasu kasashen za a mika su ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya OIM da ke da cibiya a birnin na Agadez wadda ita ce za ta dauki dawainiyar isar da su ya zuwa kasashen su.

Wani Dan kasar Najeriya da ke cikin wadanda aka koron mai suna Rabi'u da ya ce rashin isashen abinci ne ya fitar da shi daga gida zuwa kasar ta Algeriya don samun abin sakawa a bakin salati. Bakin dai sun iso garin Agadez Lafiya, sai dai sun yi kira ga gwamnatocin kaschensu da suka kara kulawa da hanyoyin kyautata rayuwar al'umominsu wanda a cewar su ta haka ne kawai za a kawo karshen irin wannan wulakanci da suke fuskanta a wasu kasashe da ba na su ba.