1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkalan Najeriya sun fara yaki sosai da cin hanci

October 3, 2017

Gwamnatin Najeriya ta nuna jin dadinta kan matakin da majalisar alkalai ta dauka na binciken wasu Karin alkalai 15 bisa zargin cin hanci. Sai dai matakin ya fara shan suka musamman membobin kwamitin bincike da aka nada.

https://p.dw.com/p/2lA1k
Nigeria Richter Korruption
Hoto: Abddulkareen Baba Aminu

A baya dai a kamen wasu manya da matsakaitan alkalai a Najeriya da nufin aike sako daga bangaren shugaban kasa da ya dauki lokaci yana zargin shari'ar da tarnaki a yakin hanci. Sai dai daga dukkan alamu tana shirin sauyawa a tsakanin alkalan da suka mika wuya a cikin wata soyayyar da ke nuna alamar kore yanzu.

Kokarin sauyin ya faro ne tare da matakin kafa wata kotu ta musamman domin yaki da cin hancin, kafin daga baya babban alkalin kasar ya sanar da wani kwamiti na musamman domin yakar hancin a cikin sashen shari'a na kasar. Na baya-bayannan na zama binciken wasu matsakaitan alkalan kasar kusan 15 da majalisar alkalai ta kasar ta kai ga sanarwa a cikin wannan mako.

Supreme Court Abuja, Nigeria
Majalisar akalan Najeriya ta sa kafar wando daya da 'ya'yanta da ke karbar na goroHoto: DW

 Tuni dai Jihar zamfara ta kai ga sallamar daya daga cikin alkalan da hukumar ke zargi da karbar na goro kafin yanke shari'a, matakan da ke dadada ran bangaren zartarwa na kasar a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin gwamnatin Najeriya.

Tun ba a kai ga ko'ina ba matakin alakalan ya fara shan suka cikin kasar da ke kallon coge musamman ma a nadin kwamiti na binciken cin hancin. Kungiyar SERAP mai bincike ga harkokin shari'a da kare mutuncin bil Adama tace kwamitin na Isa Ayo Salami ya kunshi wasu manyan lauyoyi na kasar da ake kallon na kare masu laifi ne. Barrister Baba Dala, wani lauya da ke zaman kansa a Abuja, ya ce hada tsakuwa da aya na iya illa a kokarin samar da abinci.