1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkali ya kori Saddam Hussain daga Kotu

October 10, 2006
https://p.dw.com/p/BugN

Yau ne a birnin Bagadaza na ƙasar Irak an koma saurarn shari´ar tsofan shugaban ƙasa Saddam Hussain, a zargin da a ke masa, na aikata kissan kiyasu, ga al´ummomi a zamanin mulkin sa.

Saidai alƙali, ya kori Saddam Hussain ,daga kotun, bayan wani rikici mai zafi, da su ka yi da shi, a lokacin shari´ar.

Tun daga fara wannan shari´a, ranar yau, ta kasance mafi zahi, inda ɗaya, daga muƙarban Saddam Hussain, Hussain Rachid Al-Tikriti,da shi ma ake wa shari´a, ya kai duka ga alƙali, sannan Ali Hassan Al-Majid, tsofan ministan tsaro, ya danganta alƙalan, da ƙarnan farauta, ya kuma buƙaci su yanke masa hukucin kissa, a nan take, domin ya huta da kai da koma, gaban wannan haramtata kotu.

Ta fannin tashe-tashen hankulla kuwa, an gano gawawaki 60, sannan mutane 10 su ka rasa rayuka, a yayin tarwatsewar Bom, sahiyar yau talata, a birnin Bagadaza.

A ɗaya hannun kuma, rundunar Amurika ta ce ƙarin sojojin ta 2, sun sheƙa lahira, jiya litinin a birnin bagadaza.