1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah ya yi wa Boutros Boutros-Ghali rasuwa

Salissou BoukariFebruary 16, 2016

Ofishin shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da rasuwar tsofon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Boutros Boutros-Ghali mai shekaru 93

https://p.dw.com/p/1HwM8
Boutros Boutros-Ghali ehemaliger UNO Generalsekretär
Boutros Boutros-GhaliHoto: Imago/Xinhua

Tsofon jami'in difolomasiyya dan kasar Masar Boutros-Ghali ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniya daga shekarar 1992 zuwa 1996. An haifeshi ne a birnin Alkahira kuma ya na daga cikin Kiristoci na darikar koptik. Sannan ya kasance ministan harkokin wajen Masar daga 1977 zuwa 1991.Shi ne Sakatare na farko na kungiyar Francophonie ta kasashen masu amfani da harshen Faransanci daga shekara ta 1997 zuwa 2002.

Rafael Dario Ramirez Carreno ne dai wakilin Benezuwela kasar da ke da jagorancin Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ne ya sanar da wannan labari. Boutros-Ghali wanda shi ne Sakatare na farko na Majalisar Dinkin Duniya da ya fito daga wata kasa ta Afirka, ya shirya agajin da aka kaiwa kasar Somaliya a wancan lokaci yayin da ta yi fama da matsalar yunwa.

Sai dai kuma ya sha suka dangane da rashin karfin da Majalisar Dinkin Duniya ta nuna wajen hana kisan gillan kasar Rwanda a shekara ta 1994, da kuma kasa shayo kan matsalar yakin kasar Angola.