1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah ya yiwa shahararen marubuci Naguib Mahfouz na kasar Masar Rasuwa

August 30, 2006

Takaitaccen tarihin rayuwar Naguib Mahfouz

https://p.dw.com/p/BtyR
Hoton Marigayi Naguib Mahfouz
Hoton Marigayi Naguib MahfouzHoto: AP

Naguib Mahfouz shi ne fitaccen marubuci na ƙasashen larabawa wanda ya sami karɓar lambar yabo ta Nobel a kan adabi. A ranar Talatar nan ne dai Allah ya yi masa rasuwa yana da shekaru 94 a duniya. Mahfouz wanda rubuce rubucen sa a kan batutuwa masu sarkakakiya ya karaɗe ƙasar Masar, an haife shi a watan Disambar shekarar 1911 a birnin alƙahira, kuma shi ne ɗan auta a cikin yayan mahaifin sa su shida waɗanda suka haɗa da mata huɗu da kuma maza biyu.

Yana shekaru shekaru 23 da haihuwa ya sami Degree ɗin sa na farko a kan Ilimin Falsafa a jamiár Alkahira, a dai dai lokacin da da yawa daga cikin yan Masar ɗin ke da matsayin Ilimin Primary. Ya yi aiki a gwamnatin Masar inda ya zamanto jamií mai kula da aládun gargajiya har ya zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1971.

Sau da dama ya sha tsallake rijiya da baya a hare haren da aka yi domin hallaka shi. A watan da ya gabata aka kwantar da shi a asibiti inda ya sha fama da jinya bayan da yanke jiki ya faɗi. Rahotannin da liktoci suka bayar ya yi nuni da cewa ya rasu a sakamakon kumewar jini a cikin sa.

Masharhanta da manzarta alámuran yau da kullum sun baiyana Naguib Mahfouz da cewa mutum ne wanda Allah ya yiwa baiwa da hazaka ta wallafa littafai.

Mahfouz wanda ya yi shura musamman a kan litafin da ya wallafa mai suna Cairo Trilogy ya zama gwarzo a fannin rubuce rubuce bayan da ya karkata akalar rubutun sa daga salo na gargajiya ya zuwa salo na zamananci tare da baiyana ɗabiú da aládu na tsarin masarautar Masar a ƙarni na ashirin.

Ya sami lambar yabo ta Nobel a shekarar 1988 a fannin adabi da tarihin larabawa. Ko da yake a waje guda wasu musulmi masu tsatsauran raáyi na ɗaukar sa a matsayin wanda ya kaucewa koyarwar addinin musulunci, Mahfouz ya sami kuɓuta daga wani farmaki da aka kai masa a shekarar 1994 inda aka yanke shi da wuƙa, abin da kuma ya yi masa lahani a wasu jijiyoyin sa wanda kuma ya kawo masa rauni wajen rubuce rubucen sa.

Bayan tsallake rijiya da baya da yayi daga wannan farmaki, Mahfouz ya baiyana yunƙurin hallaka shi da cewa waɗanda suka shirya wannan maƙarƙashiya, sun yi ne domin ganin bai cigaba da da baiyana haske ta wayar da kan jamaá ba.

A shekarar 1959 Al-Azahar, hukuma mafi girma ta Islama a ƙasar Masar ta haramta wani litafi da ya rubuta wanda ya yiwa laƙabi da yayan Gabalawi bisa hujjar cewa littafin ya saɓawa ƙaídojin musulunci, inda a cikin littafin ya zayyana wasu hotuna waɗanda ke kwatanci ga Allah da Manzon sa.

Mahfouz wanda ya sami ɗaukaka bayan baiyana Masar a zamanin mulkin mallaka na Britaniya da kuma mulkin kama karya na tsohon shugaban Masar Gamal Abdel Nasser ya bi sahun fitattun marubuta na sauran ƙasashen larabawa.

Mafi akasarin rubutun sa na cin karo tare da kakkausar suka daga jamián soji da shugabannin addini a Masar da ƙasashen larabawa. A cikin wani likatafi da ya rubuta a shekarar 1945 mai suna sabuwar Alƙahira, ya tattara bayanai da suka kunshi yanayin rayuwar alúma musamman mazauna birnin na Alkahira wanda marubuta suka ce ya sa samar da sabon babi a fagen adabi a ƙasashen larabawa.

Bugu da ƙari ya kuma wallafa littafi inda soki lamirin gwamnatin soji mai mulki ta wancan zamani tare da laburta tarihin ƙasar Masar bisa fahimta da raýin talakawa.

A shekarar 1960 lokacin da ba wanda ya isa ya yi kalaman batanci ga mahukunta, Mahfouz ya soki Gamal Abdel Nasser a cikin littafin sa ƙaramin zance kan kogin Nilu da Miramar.

Mahfouz ya yi ƙaurin suna tare da baƙin jini a lokacin da ya goyi bayan shirin zaman lafiya da Israila a shekarar 1979, abin da ya haifar ƙasashen larabawa da dama suka haramta littafan sa.

A ranar Alhamis mai zuwa ne idan Allah ya kai mu zaá yi janaízar sa.