1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah Ya yiwa shugaban Kosovo Ibrahim Rugova rasuwa

January 21, 2006
https://p.dw.com/p/BvBH

Shugaban lardin Kosovo Ibrahim Rugova wanda yayi fama da cutar kansa ta huhu ya rasu a yau asabar, inji jami´an Kosovo dake kurkusa da shugaban dan shekaru 62 a duniya. Wani jami´in yamma a Pristina babban birnin Kosovo ya tabbatar da rasuwar shugaba Rugova. To sai dai ya ce ka da a ambaci sunansa domin ba´a ba shi izinin ba da wannan sanarwa a bainar jama´a ba. Ibrahim Rugova wanda ke jagorantar gwagwarmayar kwatar ´yanci ´yan kabilar Albaniya daga Sabiya, a cikin watan satumban bara a hukumance aka tabbatar da kamuwarsa da cutar kansa ta huhu. Shugaba wanda ke da farin jini a tsakanin Albaniyawa ya kasance mai yawan shan taba sigari har zuwa lokacin da aka tabbatar da cutar a jikinsa. Rasuwarsa dai ta zo a wani lokaci mai daure kai ga Kosovo, wadda ke shirin fara tattaunawa ko ta karbi ´yanci ko kuma ta ci-gaba da zama karkashin yankin Sabiya.