1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Almundahanar man Iraqi...kamfaninnika sama da 50 nada hannu a ciki

October 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvNi

Rahotanni sun shaidar da cewa kamfaninnika kusan dubu hudu da dari biyar ne, keda hannu a cikin zargin da ake na gudanar da almundahana a game da shirin nan da Mdd, ta gudanar a Iraqi, wato a sayar da man ta a sayo mata abinci.

A cewar rahotannin da suka fito daga wasu kafafen yada labaru na Amurka, kasashen da wadan nan kamfaninnika suka fito da yawa daga cikin su sun hadar da Russi da Faransa.

Jaridar New york Times ta Amurka ta shaidar da cewa, kuda yake ba a fito da cikakken rahoton binciken da ake gudanarwa ba, bayanan data samu ya shaidar da cewa akwai kamfaninnika sama da sittin a duniya dake da hannu a cikin wannan almundahana.

Ana dai sa ran fitowar wannan rahoto mai shafi 500 nan bada dadewaba, a inda yayi bayani dalla dalla na kamfaninnika da kuma mutanen dake da hannu a cikin wannan ta´asa da aka gudanar a kasar ta iraqi.