Al'ummar Musulmin duniya sun soma Azumin watan Ramadan
May 27, 2017Talla
A kasashe da dama na Musulmi, irin su Jamhuriyar Nijar, da Tarayyar Najeriya al'umma sun tashi da azumi a wannan rana ta Asabar, bayan da majalisun koli na addinin Musulunci na kasashen suka tabbatar da ganin jinjirin wata.
A jawabin da ya yi wanda kuma wakilinmu na Sakkwato Faruk Mohammed Yabo ya aiko mana, mai martaba Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar na III da ke a matsayin shugaban majalisar Muslunci ta Tarayyar Najeriya ya yi kira ga jama'a Musulmi da su tashi da Azumin na Ramadan a wannan rana ta Asabar da ke a matsayin ranar daya ga wata.