1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alvaro Colom ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Guatemala

November 5, 2007
https://p.dw.com/p/C14u

An kamalla zagaye na 2 na zaɓen shugaban ƙasa a Guatemala.

Kotin Ƙoli mai kula da harakokin zaɓe ta ayyanar da Alvaro Colom na jam´iar Social Democrate a matsayin ɗan dakatar da ya lashe wannan zaɓe tare da kashi kusan 53 cikin100 ,na yawan ƙuri´un da aka kaɗa.

Alvaro Colom mai shekaru 56 a dunia, zai fara jagorancin ƙasar Guatemala ranar 14 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.

Zai gaji Oscar Berger a wannan matsayi har tsawan shekaru 4 masu zuwa.

Wannan shine karo na 3, da ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa.

Saidai har ya zuwa wannan lokaci, ɗan takara da ya sha kayi, wato Otto Perz Molina, bai fito hili ba, ya bayyana amincewa ko kuma watsi da sakamakon wannan zaɓe.