Ambaliyar ruwa a Dresden a Kasar Jamus
April 1, 2006Talla
Rahotanni daga Jihar Saxony dake gabashin Jamus sun shaidar da cewa har yanzu mutanen yankin na cikin hali na kaka ni kayi a sakamakon mummunan ambaliyar ruwa daga kogin Elbe.
Rahotanni sun nunar da cewa ambaliyar ruwan ya zuwa yanzu ta kai tsawon mita a kalla bakwai.
Ya zuwa yanzu dai bayanai sun nunar da cewa babu tabbas ko a nan gaba tunkoron ambaliyar ruwan ka iya kaiwa tsawon mita takwas ko kuma a´a.
A waje daya kuma, bayanai daga makociyar kasar ta Jamus wato kasar Czech, na nuni da cewa mutane hudu ne suka rasa rayukan su a sakamakon ambaliyar ruwan daya shafi wai yanki na kasar.