1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a Ghana

September 10, 2010

A ƙasar Ghana ambaliyar ruwa mai ƙarfi ya haddasa mutuwar mutane 17 da lalata dukiya mai yawa.

https://p.dw.com/p/P9G8
Tutar ƙasar Ghana

A ƙasar Ghana a ƙalla mutane 17 suka rasa rayukansu sanadiyar tumbatsar ruwa, bayan da hukumomin ƙasar Burkina Faso suka buɗe wani dam dake kusa da iyakarsu da ƙasar ta Ghana, a dai-dai lokacin da ake ruwan sama marka marka. Wata sanarwar da Nicolas Mensah jami'in hukumar agajin gaggawa ta ƙasar Ghana ya bayar, tace da ma ƙasar Burkina Faso ta sanar da su cewa, za ta buɗe mashigin Bagre dam, kuma ta gargaɗi mazauna kusa da yankin. Jami'in yace duk da gargaɗin da aka bayar na mutanen yankin su ƙaurace kusa da dam ɗin, amma wasu sun nuna taurin kai inda suka ci gaba da amfani da kwale-kwale don zuwa gonakinsu, domin girbin abincin da suka noma. Jami'in yace a sakamakon hakanne ruwan ya yi awun gaba da mutanen. Ruwan sama mai ƙarfi ne dai ya sa dam ɗin tumbatsa da haddasa ambaliya mai ƙarfi. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa sauyin yanayi da ke ƙaruwa, zai haddas fari da ambaliyar ruwa a yankin yammacin Afirka.

Mawallafi. Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu