1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a kasar Habasha

August 6, 2006
https://p.dw.com/p/BunZ

A kasar Habasha a kalla mutane fiye da 130 ne suka mutu a garin Dire Dawa a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda kuma ya yi awon gaba da gidaje masu yawa a gabashin kasar. Hukumar yan sanda ta kasar ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta tafkawa ya sa kogin Dechatu ya cika ya batse inda ya yi ambaliya ya kuma kwarara cikin gidaje a daren jiya a yayin da mutane suke barci. Hadin gwiwar sojoji da yan sanda wadanda ke gudanar da aikin ceto sun gano gawarwakin mutane fiye da dari daya wadanda ruwan ya yi awon gaba da su. Har ya zuwa wannan lokaci maáikatan agaji na nan na cigaba da aikin ceto domin gano wasu gawarwakin. An baiyana cewa a kalla gidaje 220 ruwan ya tafi da su. Garin Dire Dawa na tazarar kilomita 525 gabas da birnin Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.