1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a Pakistan

August 4, 2010

Mummunar Ambaliya na ci gaba da yin ɓarna a Pakistan, a daidai lokacin da ruwan sama ke ƙaruwa

https://p.dw.com/p/Oc0b
Mutanen da suka rasa gidajensuHoto: AP

A ƙasar Pakistan ƙaruwar ambaliyar ruwa na ci gaba da haddasa asaran gidaje. Ko da yau ma mutane da yawa suka mutu, kana dubban gidaje ruwean ya rusa a arewa maso yammacin asar ta Pakistan. Ambaliyar ruwan wanda ta fara tun a makon jiya, ya hallaka aƙalla mutane 1,500, yayinda ya rusa gidaje kimanin miliyan ukku. Ma'aikatan agaji sun yi gargaɗin cewa, kogunan da suka cika a yankin na iya darewa, su tumbatsa a ko wane lokaci, inda kuma ambaliyar za ta kai har izuwa kudancin ƙasar. A yankin Punjab da ke ƙasar ta Pakistan ruwa ya share ɗaruruwan ƙauyuka, kuma yanzu haka ya fara isa man'yan birane.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu