1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya

Muntaqa Ahiwa / LMJJune 30, 2016

Wata ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassa na birnin Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa a Najeriya, ta janyo asarar dukiya mai yawa.

https://p.dw.com/p/1JGyS
Matsalar ambaliyar ruwa yayin damuna a Najeriya.
Matsalar ambaliyar ruwa yayin damuna a Najeriya.Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan ambaliya dai ta lalata gidaje da gonaki dama wuraren sana'o'i da daman gaske, a wasu sassa da ke Yolan da ke zaman fadar gwamnatin jihar Adamawa, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Rahotanni sun nunar da cewa ambaliyar dai ta biyo bayan mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, da aka shafe akalla sa'o'i uku ana yi babu kakkautawa cikin dare. Wadanda abin ya fi shafa dai sune mazauna yankunan da ke da cunkoso, inda kuma ya yi barna mai yawa. Daruruwan gidaje ne dai ambaliyar ta dai-daita inda wasun su suka rurrushe kayayyakin cikinsu suka bi ruwan da ke kwarara, kasantuwar lamarin cikin dare ne ya faru. Yankunan da ambalkiyar ruwan ya fi shafa dai sun hadar da unguwar Shagari da 'Yolde Pate da ke cikin garin Yola da Mbaccure a barikin sojoji da Damilu da Jambutun Jimeta sai kuma wani bangare na unguwar Wauru-Jabbe. Haka nan ma barnar ambaliyar ta shafi wuraren sana'o'i da yawa a yankunan da lamarin ya auku. Masana kan yanayi dai na danganta ambaliyar da wasu matsalolin muhalli da sauyin yanayi da wasu ayyukan dan Adam ke haddasawa, kamar batun gine-gine ba bisa ka'ida ba da ke zama babbar matsala musamman a jihar ta Adamawa.