1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amen wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah

Yahouza S.MadobiJuly 28, 2006

Dakarun Isra´ila da na Hezbollah sun shiga kwana na 17 na yaƙi

https://p.dw.com/p/Btyq
Hoto: AP/DW

An shiga kwana na 17 a ɓarin wutar da ya ɓarke tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezbollah a kudancin Labanon.

Da sanhin sahiyar yau,rundunar Tsahal ta Isra´ila ta kai hare hare kamar yada ta saba a yankuna kudancin Labanon , inda Hezbollah ke ci gaba da turjiya ta ba mamaki.

Rahotani su nunar da cewa, masansar wutar ya fi ƙamari a Bint Jbeil da garuruwan Maroun el-Ras da ke matsayin sassanin Hezbollah.

Ya zuwa yanzu babu wata majiya mai zaman kanta, da ta bayyana mutanen da su ka rasa rayuka, da kuma assararin dukiyar da aka yi a cikin wannan gumurzu.

A jimilce, jami´an tsaron Israila sun bayana harba bamai-bamai fiye da 300 daga wayewar garin yau, zuwa yanzu, wanda su ka hallaka mutane 6, yan Labanon da kuma 1 na Jordan.

Rundunar Isra´ial,ta gayyaci mazauna garuruwan da ke kudacin Labbaon su ƙaura daga matsugunan su, mudun su na buƙatar tsira da rayuka.

To saidai da dama daga jama´ar sun yi kunnen uwar shegu da wannan kira,tare da cewar saidai a kashe tsohuwa kan daudawar ta.

A yayin da ɓangarorin ke ci gabada masanyar wuta, ta fannin diplomatia ƙasashe da ƙungiyoyin daban-daban, na dunia sun shiga yunƙurin samar da tsagaita wuta.

Domin cimma wannan buri ƙungiyar ƙasashen yankin kudu maso gabacin Asia wato, Asean a zaman taron da ta shirya a birnin Kuala-Lampour na ƙasar Malaisia, ta gayyaci ɓangarorin 2 su tsagaita wuta.

Sannan a yau ne Majalisar Ɗinkin Dunia, ke gudanar da mahaura a kann halin da ake ciki a wannan rikici.

Komitin sulhu ya bayanna bukatar tsagaita wuta, da kuma kare kadarori da rayukan jami´an Majalisar da ke aiki a yankin.

A yau ne kuma a ke ganawa tsakanin shugaba George Bush na Amurika, da abokin sa Tony Blair, wanda su ka yi ruwa su ka yi tsaki, wajen ɗaurewa Isra´ila gidin domin ta ci gaba da kai hare hare a Labanon har lokacin da yan Hezbollah su ka bada kai bori ya hau.