1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da kororon roba

Mohammad AwalNovember 21, 2010

Paparoma Benedikt na 16 ya bada damar amfani da kororon roba domin wasu keɓaɓɓun dalilai

https://p.dw.com/p/QEqU
Paparoma Benedikt na 16 wajen bukin naɗa sabbin limaman coci.Hoto: AP

A wani yunƙuri da ke nuna sassaucin ra'ayin sa, Paparoma Benedikt na 16, bayan da ya naɗa sabbin limaman cocin Katolika a fadar sa na Vatican, ya ba da damar da a riƙa amfani da kwaroron roba, domin wasu keɓaɓɓun dalilai, musamman ma wajen rage yaɗuwar cutar AIDS ko SIDA. Ana sa ran za'a wallafa waɗannan kalamai nasa a wani littafin sa da za'a ƙaddamar a ran Talata mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Littafin mai suna "Light of the World: The Pope, The Church and the Signs of Times" a turance, ya yi asali ne daga hirar da ya yi da wani ɗan jaridar Jamus mai suna Peter Seewald. Fadar ta Vatican dai ta daɗe tana hana amfani da kowace irin hanya ta kariya ko bada tazarar haihuwa da cewa ba kama kai ba ne. A halin da ake ciki yanzu, shirin Majalisar Ɗinkin Duniya ta yaƙi da cutar SIDA wato UNAIDS da sauran ƙungiyoyi masu neman kawar da cutar SIDA sun yi farin cikin wannan furuci na Paparoma kuma suna ganin shi a matsayin wani mataki da zai samar da muhimmiyar cigaba a wannan fannin.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Mohammad Nasiru Awal