1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfanin gasar ƙwallon ƙafar duniya

April 10, 2010

A yayin da ya rage kimanin watanni biyu a fara gasar cin kofin Duniya a fagen ƙwallon ƙafa a Afirka ta Kudu har yanzu jama'a na ta cece - kuce akan matsalolin da suka dabaibaye shirye-shiryen gasar

https://p.dw.com/p/MshU
Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar Afirka Ta KuduHoto: picture alliance / dpa

Matsalolin da suka shafi baƙuncin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin Duniyar da ƙasar Afirka ta kudu za ta karɓa a ranar 11 ga watan Yuni dai, sun haɗa da tsadar farashin tikitin shiga dandalin wasannin, da hana masu ƙananan sana'ao'i gudanar da harkokin su a kusa da filayen wasannin, da kuma yawan yajin aikin da ma'aikatan gina filayen suka yi ta shiga - lamarin daya sa wasu ke dasa a'yar tambayar, ko ma akwai gajiyar da ƙasar zata samu daga karɓar baƙuncin gasar, duk kuwa da cewar, wasu mutanen ƙasar na yin farin cikin damar da ƙasar su ta samu.

"Wannan mutumin dai cewa yake: Ina mai matuƙar farin cikin cewar kowa zai amfana daga wannan damar, ƙwarai kuwa hatta masu ƙanana da manyan sana'oi ma zasu amfana, ƙwarai!"

Wannan matar ma ga abin da take faɗi:

"Ina farin ciki sosai. Ina ganin akwai abubuwa da dama da zasu sauya a ƙasarmu."

'Yan ƙasar Afirka ta kudu da dama dai na nuna jin daɗin su game da gasar cin kofin Duniya na ƙwallon ƙafar da ƙasar su za ta karɓi baƙuncin ta, amma kuma akwai waɗanda ke ɗari - ɗari da hakan. Akwai mutanen ƙasar da hukumomi suka tayar dasu daga matsugunansu ba tare da biyan su kuɗaɗen fansa ba, ga shi kuma gwamnati ta ce, masu ƙananan sana'oi a titunan dake kusa da dandalin wasannin, su ma ba zasu sami damar yin hakan ba. Nkosinathi Paul Jikeka, mai fafutukar kare haƙƙin masu sana'a akan titi ne:

"Sakamakon nacin da hukumar ƙwallon ƙafa a Duniya ta yi, mutanen da suka shafe shekara da shekaru suna yin sana'oinsu a manyan filayen wasannin, a yanzu an hana su, kuma ma ba zasu iya zuwa ko da kusa da filayen ba. An keɓe wuraren ne ga manyan kanfanoni - irin su McDonalds, Coca - Cola da dai irin kamfanonin nan dake da nasaba da Turai."

To, sai dai ba wai masu sana'oi akan tituna ne kaɗai matsalar ta shafa ba, su ma ma'aikatan gina manyan filayen wasannin, suna fama da tasu fafutukar:

Ma'aikatan ginin filayen dai, sun gudanar da yajin aiki har sau 26, akan matsalolin da suka shafi sufuri zuwa wurin aiki, kula da lafiyar su, kana a baya bayan nan tunda an kammala gina manyan filayen wasannin guda 10, galibin ma'aikatan, waɗanda yawansu ya kai dubu 70 ba su da aikin yi.

A cewar Eddie Cottle na ƙungiyar adalci a lokacin wasa, kuma adalci ga kowa, wadda ke kare haƙƙin ma'aikatan, akwai wata matsalar da ta rage:

"Babu wata Inshora ta musamman da aka ware domin rashin aikin yi, kuma ma'aikatan sun yi hasashen tsunduma cikin fagen marasa aikin yi, bayan kammala gini, saboda hakane suke fafutukar ganin hukumomi sun ware musu kaso cikin kuɗaɗen shigar da za su samu daga wasannin."

Hakanan kuma da dama daga cikin 'yan ƙasar na da ra'ayin cewar, hanya ɗaya tilo ta haɗa kan al'ummar ƙasar, ita ce, kowa ya ci gajiyar albarkatun da Allah ya hore mata, ba wai ta hanya karɓar baƙuncin gasar ƙwallo ba.

Duk da cewar, ginin filayen wasannin ya kammala, amma har yanzu 'yan ƙasar na ci gaba da tambayar, wai shin wanene ma zai ci gajiyar baƙuncin gasar ƙwallon ƙafar da Afirka ta kudu zata karɓa a 2010 ne?

Mawallafa: Chiponda Chimbelu/Saleh Umar Saleh

Edita: Mohammad Nasiru Awal