1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Ana cigaba da jimami game da harin Orlando

Ahmed SalisuJune 13, 2016

Gwamnatin Amirka da kungiyoyi na Musulmi a ciki da wajen Amirka na cigaba da yin Allah wadai kan harin da aka kai wani gidan rawa na 'yan luwadi a birnin Orlando.

https://p.dw.com/p/1J5U0
USA Schießerei in Orlando zahlreiche Tote Nightclub Pulse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Burbank

Yayin da jami'an tsaro ke cigaba da yi bincike kan harin nan na gidan rawa na birnin Orlando inda masu neman jinsi guda ke haduwa, ana cigaba da yin Allah wadai game da wannan hari wanda Amirka din ba ta taba ganin irinsa ba.

Hukumomi a birnin Orlando na Amirka sun fara bayyana sunaye da shekarun mutanen da harin na wani gidan rawa na masu neman jinsi guda ya rutsa da su a karshen mako. Wata majiya a birnin na Orlando ta ce yanzu an fidda sunayen mutane goma wanda shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 37 kuma ma tuni aka sanar da 'yan uwansu kana nan gaba za a cigaba da sanya sunayen sauran mutanen a shafin intanet mallakar hukumomi a birnin.

Al'ummar Amirka da ma na sauran sassan duniya gami da kungiyoyi na Musulmi na cigaba da yin Allah wadai da harin da aka kai kan wadannan mutane a gidan rawar na masu neman jinsi guda wanda shi ne mafi muni da aka taba gani a Amirka din. Jami'an tsaro dai sun bayyana sunan Omar Mateen dan shekaru 29 da haihuwa wanda ke da asali da Afghanistan amma aka haifa a Amirka da kai wannan hari, kuma mutumin ya bayyana mubayi'arsa da kungiyar nan ta IS da ke son girka daular Islama a Siriya da Iraki.