1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Austreliya sun ce za su ja damara wajen yakan matsalar gurbacewar yanayi.

January 12, 2006
https://p.dw.com/p/BvCg

Amirka da Austreliya sun dau alkawarin ba da kudi kimanin Euro miliyan dari don aiwatad da wani shirin yankunan Asiya da na Pacific, na rage hayaki mai janyo dumamar yanayi da masana’antu ke fitarwa. Amma masu fafutukar kare kewayen bil’Adama, sun ce wannan alkawarin, babu wani muhimmin sakamakon da zai haifar, ban da karfafa wa masu gurbata yanayi gwiwa. Sun dai yi kira ga mai da hanakali kan tushen samad da makamashi mai sabuntuwa kamar rana ko kuma iska, wanda kuma za a iya dogara a kansa. Amirkan da Austreliya da wasu kasashe 4 na Asiyan, a cikinsu har da Sin da Indiya ne, ke halartar wani taro kan batun lalacewar yanayi a birnin Sydney. Duk kasashen dai sun yarje kan cewa, kona man fetur na cikin ababan da ke janyo dumamar yanayi, amma ba za su iya kaucewa daga yin amfani da wannan hanyar samad da makamshi ba, saboda tattalin arzkinsu ma ya dogara ne kacokan a kanta.