Amirka da Faransa na kokarin cimma matsaya daya akan kudurin Libanon
August 5, 2006Faransa da Amirka sun kusa cimma matsaya daya a kokarin da suke yi na amincewa da wani daftarin kuduri kan yankin GTT. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka Sean McCormack ya ce bangarorin 2 na kusantar juna yayin da abokin aikin sa Tom Casey ya yi fatan cewa za´a amince da kudurin a farkon mako mai zuwa. Jakadun kasashen biyu a MDD, Jean-Marc de la Sabliere da John Bolton sun gana har sau uku a jiya juma´a a kokarin warware bambamce bambamce da ke tsakaninsu. Bolton ya nunar da cewa ana samun ci-gaba a tattaunwar da suke yi.
Bolton ya ce:
“Da mu da Faransa mun kuduri aniyar cimma tudun dafawa akan wannan batu. Yana da muhimmanci idan muka yi kokarin cimma yarjejeniya kamar yadda muka saba yi a lokutan baya. Ko tantama babu, zamu fitar da wani kuduri da zai samu karbuwa ga kowa da kowa.”