1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Jamus za su tsaurara dokokin hada hadar kuɗi

May 27, 2010

Jamus da Amirka za su yi huɓɓasa wajen warware rikicin kuɗin da wasu ƙasashe ke fama da shi

https://p.dw.com/p/NYoc
Hoto: BMF/Jörg Rüger

Ministan kula da harkokin kuɗi a Jamus Wolfgang Schäuble, da takawaran aikin sa na ƙasar Amirka Timothy Geithner, sun bayyana ƙudurin da ƙasashen su ke da shi na ganin sun samar da tsauraran ƙa'idoji ga kasuwannin dake tu'ammuli da kuɗi a duniya. Ministocin biyu waɗanda suka kammala wata ganawar da suka yi a birnin Berlin na nan Jamus sun taɓo batun yadda tarayyar Turai ke ƙoƙarin warware matsalar bashin da ta yiwa wasu ƙasashen yankin ka'tu'tu.

A lokacin da yake yiwa taron manema labarai jawabi bayan ganawar, sakataren kuɗin Amirka Timothy Geithner ya bayyana cewar, hukumomi a birnin Washington na ƙasar Amirka na ƙaunar ganin an samar da ƙa'idoji masu tsauri ga cibiyoyin kuɗi. Shi kuwa Wolfgang Schäuble, gargaɗi ne ya yi na cewar, akwai buƙatar duniya ta samar da tsauraran dokoki ga abubuwan da suka shafi hada hadar kuɗi. Yana mai cewar, matsayin da Amirka da Jamus suka ɗauka game da batun ya yi kusa da na juna- fiye da yadda ake gani a zahiri.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu