1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da tarayyar Turai sun goyi bayan kawad da shingaye ciniki a duniya

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOq

Amirka da KTT sun goyi da bayan daukar karin matakan sakarwa harkokin kasuwancin duniya mara. Bayan wani taro da suka da shugaban Amirka GWB a fadar White House shugaban hukumar kungiyar EU Manuel Barroso ya ce ra´ayi ya zo daya dangane da samar da walwala, wanzuwar demukiradiyya da kuma kare hakin dan Adam. Shi kuwa a nasa bangaren Bush kira yayi ga kasashen Turai da su kara bude kofofin kasuwannin su musamman na kayan amfanin noma. To sai dai tun da farko gwamnatin Faransa ta nu a adawa da wannan mataki. Gwamnatin birnin Paris dai na fargabar asarar dinbim kudaden shiga ga manoman Faransa. A gobe laraba za´a fara wani zagaye na gaba akan harkar kasuwancin duniya a birnin Geneva. Daga cikin batutuwan da za´a fi mayar da hankali akai sun hada da kudin tallafi da ake ba manoma.