1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Matakin takaita yawaitar bindigogi

Gazali Abdou TasawaJanuary 5, 2016

Shugaba Obama ya bayyana cewa dole duk wanda ke saida bindigogi ya nemi lasisi, kuma gwamnati za ta sa ido wajen ganin an yi aiki da dokokin kasar kan batun bindigogi.

https://p.dw.com/p/1HYxx
USA Waffengesetz Waffenbesitz
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Lo Scalzo

Shugaban Amirka Barack Obama ya jaddada muhimmancin gaggauta amfani da dokar sa ido kan harakokin cinikayyar bindigogin a kasar Amirka a wani mataki na kawo karshen harebe-harben da ke wakana a kasar. Shugaba Obama ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron manema labarai da ya gudanar a Yammacin wannan Talata a fadarsa ta White House.

Shugaba Obama ya ce duk wanda ke saida bindigogi dole ya nemi lasisi sannan na biyu za a tabbatar ana aiki da dokokin da ke da akwai sannan gwamnati za ta taimaka wa wadanda ke fama da tabin hankali da yawanci ke amfani da bindigogin wajen kisan jama'a.

Sabuwar dokar da Shugaba Obama ke son yin gaban kansa wajen soma amfani da ita bayan da ya jima yana fiskantar turjiya daga 'yan majalisar dokokin kasar ta tanadi tsaurara matakan bayar da lasisin sayar da bindigogi dama tantance mutanen da suke sayen bindigogin nasu har ta hanyar internet.

Haka zalika matakin ya tanadi hukuncin dauri na shekaru biyar da tarar kudi Dalar Amirka dubu 250.