1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na bukatar a tsagaita wuta a Siriya

Abdourahamane Hassane
March 12, 2018

Amirka ta gabatar da wani daftarin kudiri a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na nema a tsagaita barin wuta.

https://p.dw.com/p/2uCd2
USA UN Sicherheitsrat Nikki Haley
Nikki Haley jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/newscom/J. Angelillo

Jakadiyar Amirka a Majajalisar ta Dinkin Duniyar Nikki Haley wace ta bayyana kudirin ta soki lamirin Rasha da Siriya da gaza aiwatar da yarjeniyar dakatar da bude wutan da aka cimma a makonin da suka gabata. Babban magatagarda na MDD Antonio Guterres ya ce akwai bukatar gaggawa ta isar da kayan agaji na jin kai a gabashin Ghouta.