1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na cikin ƙasashen da ke take hakkin 'yan jaridu a duniya, inji "Reporter Sans Frontière".

YAHAYA AHMEDOctober 24, 2006

Ƙungiyar nan mai fafutukar kare hakkin maneman labarai "Reporter Sans Frontière" ta buga jerin sunaye na ƙasashen duniya, wanda ya fara daga ƙasar da ta fi kare 'yancin maneman labarai har zuwa wadda ta fi kowacce yi wa 'yan jaridu danniya da kama karya.

https://p.dw.com/p/Btxc
Alamar take hakkin maneman labarai.
Alamar take hakkin maneman labarai.Hoto: picture-alliance / dpa

A cikin wani rahoton da ta gabatar game da wannan jerin sunayen, ƙungiyar ta yi suka ga wasu ƙasashen dimukraɗiyya na yamma, waɗanda su ne ma ke kambama kansu da kare hakkin ɗan Adam.

Tun ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2002 ne aka sami sauyi a harkokin yaɗa labarai a duniya. Ƙungiyar “Reporter Sans Frontière“, wadda ta gabatad da rahotonta na shekara-shekara a birnin Paris, ta ce saboda barazanar ta’addanci da ƙasashen yamma masu mulkin dimukraɗiyya ke huskanta, an sami wani yanayi inda a waɗannan ƙasashen ma, ake ta ƙara take hakkin maneman labarai. Kamar dai yadda kakakin ƙungiyar ta bayyyanar, gwamnatoci kamarsu na Amirka, sun sha yunƙurin tilasa wa maneman labarai su ba su tushen wasu labaran da suka buga kan wasu batutuwan da ba masu faranta rai ba ne gare su. Kakakin ta ƙara da cewa:-

„Irin waɗannan halayen dai ba su dace ba, musamman ma ga Amirka. A cikin jihohi guda 17 na ƙasar, an soke kariyar da ake bai wa maneman labarai, abin da ya sanya su cikin wani mawuyacin hali wajen buga rahotanninsu. A ko yauushe suna huskantar barazana, ko da ma binciken da suka gudanar wajen buga rahotannin ba su shafi ta’addanci ba. Akwai dai wani lokaci, inda aka kame wani ɗan jarida sabosa ya ƙi miƙa hotunan bidiyo da ya ɗauka ga hukumomin tsaro na Amirkan. Kazalika kuma an tsare ’yan jaridu a sansanin Guantanamo da kuma Iraqi. Duk wadannan dai na nuna take hakkin maneman labarai a Amirkan, kuma ƙungiyar ta yi la’akari da su wajen buga rahoton nata.“

A wannan shekarar ma dai Amirka ta yi ƙasa ƙasa a jerin ƙasashen da ƙungiyar Reporter Sans Frontière ta ce suna cikin waɗanda suka fi take hakkin maneman labarai. Ita ce dai a jeri na 53.

Ba dai gwamnatoci da hukumomi kawai a ƙasashen dimukraɗiyyar Yamman ne ƙungiyar ta ce suna angaza wa maneman labarai ba, har da ma mutane ɗai-ɗai masu shirin afka wa maneman labaran. A lal misali a ƙasar Denmark. A shekarar bara, ita ce a matsayi na farko a jerin da ƙungiyar ta buga. Amma a wannan shekarar, sai ga shi ta yi ƙasa zuwa matsayi na 19. Dalilin haka kuwa, shi ne zanen ɓatanci ga annabi Muhammadu, tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi, da aka buga a wata jaridar ƙasar. Kamar dai yadda kakakin ƙungiyar Reporter Sans Frontière, Elke Schäfter ta bayyanar:-

„Bayan buga wannan zanen a jaridar, an sami mutane da yawa a ƙasar da suka afka wa wasu jaridu da ma yi musu barazana, har ma ya kai ga bai wa wasu maneman labaran ƙasar jami’an tsaro masu kare lafiyarsu. Wannan kuwa ya auku ne a ƙasar dimukraɗiyya ta Yamma, mai kambama kanta da kare hakkin ɗan Adam.“

A nan Jamus ma dai, an yi wa wasu gidajen buga jaridu barazanar kisa, saboda buga hotunan wannan zanen ɓatancin. Amma ƙungiyar Reporter Sans Frontière ta yi kakkausar suka ne ga matakan da hukumomin tsaron Jamus suka ɗauka na sa ido kan da kuma bin diddigin yadda wasu maneman labarai ke gudanad da ayyukansu. Wannan lamarin dai ya sa matsayin Jamus ma a jerin ƙasashen da ƙungiyar ta buga, ya yi ƙasa, ta faɗo daga matsayi na 18 a shekarar bara zuwa matsayi na 23. Kai har ƙasar Bosniya ma ta ɗara Jamus a wannan mizanin. Elke Schäfter ta ce an sami kyakyawar yanayi a harkokin aikin maneman labarai a ƙasar a shekarun bayan nan:-

„A cikin shekaru biyun da suka wuce, an sami ’yancin walwala a huskar aikin jarida a ƙasar. Ana iya ganin sakamakon hakan dai a jerin da muka buga.“

Ita dai ƙasar ta Bosniya, a wannan shekarar, ta zo ne a matsayi na 19 a jerin ƙasashen da ƙungiyar ta buga a rahotonta. Ko wannan na nufi ke nan cewa, maneman labarai na da ’yanci a Bosniyan fiye da Jamus? A ganin Elke Schäfter dai:-

„A’a ba haka lamarin yake ba. A jerin namu dai, ƙasashen da ke daga matsayi na ɗaya zuwa matsayi na 30 na da yanayi, wanda za mu iya cewa, ya dace da aikin mamenan labarai, kuma masu zaman kansu. Amma a wasu ƙassashen, akwai bukatun gyara.“

Ƙasashen da ke ƙasa ƙasa a kan wannan mizanin sun haɗa ne da Sin, da Myanmar da Kuba da Turkmenistan da Eritrea. Amma duk waɗannan ƙasashen, suna gaban Korea Ta Arewa, wadda ita ce ƙungiyar ta ce zakarar take hakkin maneman labarai a duniya. Game da halin da ake ciki a ƙasar dai, Elke Schäfter ta bayyana cewa:-

„Ana matuƙar sa ido kan kafofin yaɗa labarai a wannan ƙasa. Duk wani ɗan kuskure, ko da ma na rubutu ne, zai iya sa a ɗaure mutum, wai don horad da shi, ya sami ƙwarewa game da yadda zai dinga buga rahotanni da ababan da ya kamata ya yi la’akari da su.“