1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na gindaya wa shirin yi wa kafofin Majalisar Dinkin Duniya garambawul shinge.

YAHAYA AHMEDAugust 26, 2005

Bisa dukkan alamu dai, Amirka na shirin hana ruwa gudu a hidimomin da ake yi na yi wa kafofin Majalisar Dinkin Duniya garambawul. Jakadanta a Majalisar, John Bolton, ya gabatad da canje-canje kusan dari 5, da yake son ganin an yi wa tsarin shirin da Kofi Annan ya gabatar.

https://p.dw.com/p/BvaB
Tutar Majalisar Dinkin Duniya
Tutar Majalisar Dinkin DuniyaHoto: AP

Kai tsaye dai, Amirka na son share duk wani sakamakon da Majalisar Dinkin Duniya ta cim ma a shekarun baya, wanda kuma take alfahari da shi. A lal misali kaddamad da burin nan na wannan karnin, wanda ya tinkari rage yawan talauci a duniya zuwa rabin adadinsa na shekara ta dubu 2 kafin shekara ta 2015, ko kuma yarjejeniyar ta Kyoto wadda ta tanadi rage dumamar yanayi don shawo kan annoba iri-iri da dumamar ke janyo wa muhalli, abin da kuma ke haddasa asarar rayuka da kadarori a yankuna daban-daban na duniya, ko kuma batun kafa kotun nan ta kasa da kasa, wadda za ta iya hukuntad duk wani mai aikata laifi, ba tare da yin la’akari ko daga wace kasa yake ba. To duk wadannan, Amirka ta ce ba ta son ganin sun sami shiga cikin shirin garambawul da ake niyyar yi wa kafofin Majalisar Dinkin Duniyar. A daura da haka, ta gabatad da nata bukatu kusan dari 5, wadanda take son ganin an amince da su, inda kuma take nanata cewa, a yarje kan bukatun nata cikin gaggawa saboda lokaci na kurewa.

Wannan matsayin da Amirkan ta dauka dai, ba abin mamaki ba ne. Saboda tun da ma can tana nuna rashin amincewarta a fakaice, ga muhimman jigogin shirin na Majalisar Dinkin Duniya. Tana kambama kanta ne saboda kasancewarta kasar da ta fi ko wacce biyan mafi yawan kudaden gudummuwa ga Majalisar. Amma wai shin, hakan ya ba ta dama ke nan ta cusa wa duk duniya ra’ayoyinta da kuma bukatar a goyi bayansu ?

A halin yanzu dai kamar haka lamarin yake son ya kasance. Saboda ita Amirkan dai tana daukan matakan da gamayyar kasa da kasa ta yarje a kansu ne ta yadda tag a dama, amma ba kamar yadda aka tsara wa kowa ba. A lal misali, ta ba da sanarwar kara kudaden da za ta kashe wajen ba da taimakon raya kasa, amma ba bisa ka’idojin da Majalisar Dinkin Duniyar ta yarje a kansu ba. A jihohi da dama na Amirkan kuma, ana daukan matakan kare muhalli da rage yawan hayakin Carbon dioxide da masana’antu da ababan sufuri ke fitarwa, wadanda ke janyo dumamar yanayi. Amma gwamnatin fadar White House na yin hakan ne ta yadda ta ga dama, ba ta kiyaye ka’idojin yarjejeniyar Kyoto da aka cim ma ba. Kazalika kuma, gwamnatin shugaba Bush, ba ta sha’awar amincewa da rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kotun kasa da kasa, saboda a nata ganin, masu gaba da Amirka za su iya yin amfani da wannan dama don daukaka kararraki game da ita a kotun. Amma a inda bai shafe ta ba, ta yi amanna da shawarar mika batun yankin Darfur ga kotun na birnin Den Haag.

Ko yaya al’amura za su kasance nan gaba dai, Amirka na son ganin nata burin ne aka fi bai wa muhimmanci a Majalisar Dinkin Duniyar. Ba batun fadada kwamitin sulhu ne ya dame ta ba. Tana son duk duniya ta goyi bayan manufarta ne ta abin da take kira yaki da ta’addanci da kuma hana yaduwar makaman kare dangi. Wadannan jigogin dai, ba su sami wata muhimmiyar ambata a tsarin shirin da Kofi Annan ya gabatar ba.

A halin yanzu dai, jami’an diplomasiyya a birnin New York na huskantar wani gagarumin kalubale ne, kafin taron koli na Majalisar dinkin Duniya, wanda za a yi a cikin wata mai zuwa. Saboda ya kamata su yi bitar duk kundin shirye-shiryen garambawul din da ake son yi wa kafofin majalisar, kafin wannan lokacin.

Masharhanta dai na ganin cewa, ba zai yiwu a ce an soke batun burin wannan karnin, da na yarjejeniyar Kyoto da kuma na kafa kotun kasa da kasa daga shirin garambawul din ba. Saboda hakan, zai alamta yin watsi ke nan da duk muhimman nasarorin da Majalisar Dinkin Duniya ta samu a cikin `yan shekarun baya da suka wuce.

Za a iya dai cim ma wata madafa, idan ana so, inda za a nanata muhimmancin yaki da ta’addancin da hana yaduwar makaman kare dangi a cikin kundin Majalisar Dinkin Duniyar. Amma sai kuma a bar duk sauran ka’idojin kamar yadda suke. A ganin masharhanta dai, hakan zai iya bai wa gwamnatin birnin Washington alamar cim ma burinta.