1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na girmama addinai daban-daban

August 14, 2010

Obama ya bada goyon bayan gina sabon masallaci a New York

https://p.dw.com/p/Ons0
Shugaba Barack Obama na AmirkaHoto: AP

Shugaban Amirka Barack Obama ya baiyana amincewar sa da gina wani masallaci a birnin New York ta Amirka. A wani jawabi a lokacin cin abincin buɗe baki da wasu Amirkawa musulmai a fadar white House, Obama ya bayyana yancin da kowace al'uma keda ita na gudanar da addini ba tare da tsangwama ba, kamar dai yadda yake ƙunshe a kundin tsarin mulkin Amirka shekara da shekaru.

Obama yace- Amirkawa munyi imani da 'yancin addini. kuma kowa yana da 'yancin gudanar da addinin sa, a wannan ƙasa ba tare da tsangwama ba, don haka gwamnatin mu ba za ta nunawa kowa ban-banci ba.

Tuni dai masu suka ga matakin gina masallacin da kuma makarantar Islamiya a kusa da harabar da aka kai harin 11 ga watan satumba, suka baiyana kalaman na shugaba Obama da cewar cin fuskane ga wayan da suka rasa rayukan su a harin na birnin New York.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Abdullahi Tanko Bala