1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMIRKA NA SHA'AWAR HARKAR MAN FETUR A YAMMACIN AFIRKA

YAHAYA AHMEDJune 8, 2004

Yayin da shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ke halartar taron kasashen G-8, rundunar sojin Amirka ta fara wani dauki da mayakan ruwanta a gabar tekun Afirka ta yamma. Wannan rawar daji a teku da rundunar ke yi, wato wani shiri ne da Amirkan ta sanya a gaba, na nuna cewa, duk da gwagwarmayar da sojojinta ke yi a Iraqi, har ila yau dai a ko’ina a duniya sai an dama da ita.

https://p.dw.com/p/Bvj3
Irin manyan jiragen da ke jigilar man fetur daga Afirka Ta Yamma zuwa nahiyar Turai da kuma Amirka.
Irin manyan jiragen da ke jigilar man fetur daga Afirka Ta Yamma zuwa nahiyar Turai da kuma Amirka.Hoto: AP

Ba haka kawai ne Amirka ta zabi inda za ta nuna karfin sojinta ba. Gabar tekun Afirka ta Yamma, wadda aka fi sani da suna Gulf of Guinea a turance, yanki ne mai arziki gaske. Kusan a ko’ina a yankin, an gano tushen man fetur a cikin `yan shekarun da suka wuce. A galibi kuma, ana hakon man ne a cikin tekun kasashen yankin, wato aikin da aka fi sani da suna Offshore a turance. Wannan bangaren hakon man, wato daga karkashin kasa amma a cikin teku, fasaha ce mai tsada, amma kuma tana da fa’idoji. Kamfanonin da ke hakon man a teku, ba sa huskantar rikikici, kamar irin gwagwarmayar masu hakon man kan kasa ke yi da mazauna yankunan da suke aikin. Game da Najeriya alal misali, mazauna yankin Niger-Delta, kullun gwagwarmaya suke yi da masu hakon man fetur a yankin. In ko a can cikin teku ne, wannan matsalar ba ta tasowa ma. Kamar dai yadda Lutz Neumann, wani jami’in kungiyar nan ta Afirka-Verein ta nan Jamus, wadda ke kula da harkokin da kamfanonin Jamus ke yi a nahiyar Afirka, ya bayyanar:-

"Musamman ga Najeriya dai, wannan fasahar na fa’ida ainun. Duk kamfanonin da ke hakon mai a cikin teku, to da gwamnatin tarayya kawai suke ma’ammala. Amma duk masu hakon mansu a kan kasa kuwa, sai kuma sun sasanta da gwamnatocin jihohin da suke aikin, da kuma mazauna yankunan da ake hako man."

Tun shekaru da dama ne dai aka gano tushen mai a yankin gabar tekun Afirka Ta Yamma, da ma a cikin wasu kasashen da ba su da tekun. A halin yanzu, a kasashe kamarsu Cadi, da Sudan da Angola, da Equitorial Guinea, da Tsibiran Sao Tome da Principe, duk ana hako man fetur. Duk inda dai ake da man fetur, to babu shakka, ko ta yaya sai an sami kasancewar Amirkawa a gun.

A kasar Equtorial Guinea, tun shekaru da dama ne ake gudanad da mulkin kama karya, inda kuma mahukuntan kàsar ba su damu ma da tsara shirin raya kasar ba, duk da arzikin man fetur da take da shi. A cikin kusan duk fadin kasar, babu wani titi ingantacce. Amma sai ga shi shekarar bara, dan shugaban wannan kasa ya sayo motar nan ta Rolls Royce, wadda ita ce ta farko irinta a kasar, yana ta sharholiyarsa da ita.

Su dai kamfanonin hakon man daga kasashen Yamma, babu abin da ya fi damunsu, sai dimbin yawan ribar da za su dinga kwasa daga Afirka. Ana ganin dai cewa, hakon man a Afirka Ta Yamma, ya fi janyo musu fa’ida. Daga gabar tekun Afirka Ta Yamman dai, za su iya yin jigilar mansu a sawwake zuwa Amirka ko kuma Turai, ba tare da kashe dimbin yawan kudade kamar yadda za su yi daga tekun Parsha ba alal misali. Bugu da kari kuma, mafi yawan kasashen Afirka masu man fetur din, ba sa cikin kungiyar nan ta OPEC. Sabili da haka, farashinsu yana kasa kasa da na kungiyar OPEC din.

Kawo yanzu dai, arzikin man fetur da kasashen Afirkan ke da shi bai janyo wa al’ummominsu wata wadata ko ci gaba ba. A lal misali duk da arzikin da kasashe kamarsu Gabun ko kuma Najeriya ke samu daga harkar man fetur, mafi yawan al’ummansu, sai kara talaucewa suke yi. A kasar Sao Tome ma, gano man fetur din ne ya janyo yunkurin juyin mulkin da aka yi. Wasu rahotanni kuma nan nuna cewa, shugaban mulkin kama karya na Equitorial Guinea, duk kudin man fetur da kasarsa ta sayar, yana jibge su ne a ajiyar bankinsa a Amirka. A kasar Cadi, bankin duniya ta shimfida wa gwamnatin kasar wasu ka’idoji, na kashe kudaden da ake samowa daga cinikin man kai tsaye, a shirye-shiryen raya kasa. Kawo yanzu kuwa, rahotanni na nuna cewa, ba a cim ma wani abin a zo a gani ba a kasar. Farkon kudin shigar da kasar ta samu daga harkar man fetur, gwamnatin ta yi amfani da shi ne wajen sayo makamai.