1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce Iran na fuskantar ƙarin takunkumi

May 18, 2010

Ƙasashen yammacin duniya na tsara irin ƙarin takunkumin da za su sanyawa Iran

https://p.dw.com/p/NRLn
Hoto: AP/AP Montage

Manyan ƙasashen yammacin duniya sun cimma daidaito akan wani daftarin ƙudurin sanyawa ƙasar Iran ƙarin takunkumi bisa shirin niukiliyar ta, wanda ake takaddama akansa. A lokacin da take bayar da sanarwar hakan a birnin Washington na ƙasar Amirka, sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, ta bayyana cewar, daftarin da aka tsaran, ya sami goyon bayan ƙasashen Rasha da China. Ta kuma ƙara da cewar, a wannan Talatar ce, ake rarraba daftarin ga ɗaukacin mambobin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya. Wannan daftarin kuma ya yi watsi kenan da yarjejeniyar da ƙasashen Brazil da Turkiyya suka cimma tare da Iran, wadda ta tanadi cewar, Iran za ta aika da wani ɓangare na sanadarin Uranium ɗinta zuwa ƙetare domin sarrafa shi.

Mrs Clinton, ta ce matakin da suka ɗauka, amsa ce ga daidaiton da aka samu a tsakanin Iran da Turkiyya da kuma Brazil, inda ta ambata cewar,

" A ganina, wannan sanarwar, cikakkiyar amsa ce ga ƙoƙarin da mahukunta a birnin Tehran ke ta yi a 'yan kwanakin baya bayannan, wadda za mu iya bayarwa."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal