1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya, wani babban yaƙi ne tsakanin ’yan ta’adda da masu fafutukar neman ’yantad da yankin.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoL

Shugaba Bush na Amirka, ya ce rikicin da ake yi a halin yanzu a Gabas Ta Tsakiya, wato wani gagarumin ɗauki ne da masu fafutukar neman ’yantad da yankin gaba ɗaya suka sanya a gaba, na yaƙan kafofin danniya, da kama karya da ta’addanci, waɗanda tun shekaru da dama suke ta cin karensu babu babbaka a wannan yankin.

Shugaba Bush ya yi wannan jawabin ne yayin wata ziyarar da ya kai a birnin Miami a jihar Florida. Amirka dai, inji shi, za ta kasance ne a ɓangaren masu yaƙi da ta’addanci:-

„Rikicin da ake yi yanzu, wata babbar gwagwarmaya ce tsakanin masu neman ’yanci da walwala da kuma masu bin tafarkin ta’addanci a yankin Gabas Ta Tsakiya. Tun shekaru da dama dai, halin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiyan ya bai wa ’yan kama karya da ta’addanci damar cin karensu babu babbaka, abin da ya janyo harin da aka kawo wa Amirka a ran 11 ga watan Satumba. To ya kamata a canza wannan halin da ake ciki. Dalilin da ya sa ke nan Amirka ke yaƙan magoya bayan ta’addanci, take kuma yunƙurin kafa tafarkin dimukraɗiyya a duk faɗin yankin na Gabas Ta Tsakiya. Wannan dai ba karamin aiki ba ne, kuma ba aiki mai sauƙi ba ne. Amma aiki ne da ya zamo wajibi gare mu.“