1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Hana shiga jirgin sama da wasu na'urorin komfuta

March 21, 2017

Jami'an Amirka sun sanya takunkumi kan wasu na'urorin da fasinjoji kan shiga da su cikin jirgin sama daga kasashen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/2Zfic
USA Sicherheitskontrollen Hartsfield-Jackson Atlanta International Airport
Hoto: picture-alliance/dpa/E. S. Lesser

Matafiya jiragen sama daga wasu kasashen da Musulmi ke da rinjaye ba za a yarda su shiga Amirka da manyan na'urorin tafi da gidanka a cikin jakunansu na hannu ba. Mahukuntan Amirka sun ba da dalilin daukar wannan matakin na hana rike wasu na'urorin kamar Notebook ko Laptop da barazanar kai hare-hare. Wannan haramcin ya shafi jiragen sama daga filayen jiragen sama guda 10 a kasashe takwas. Airport din sun hada da na Atatürk da ke birnin Santambul da na Doha da Abu Dhabi sai kuma filin jirgin saman birnin Alkahira. Yanzu an ba su wa'adin kwanaki hudu da su fara aiwatar da wannan haramci.

Tun a daren Litinin zuwa wayewar gari a wannan Talata kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Saudi Airlines da Royal Jordan suka wallafa labarin haramcin a shafinsu na Twitter, amma daga baya suka goge, saboda jita-jitar cewa sun yi riga malaman masallacin wajen bayyana labarin.