1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMIRKA TA JANYE JAKADIYARTA DAGA KASAR SIRIYA.

Yahaya AhmedFebruary 16, 2005

Amirka ta ba da sanarwar kiran jakadiyarta a birnin Damascus zuwa gida a can birnin Washington, don gudanad da abin da ta kira SHAWARWARI NA GAGGAWA. Ita dai gwamnatin Bush ta fara daukan wani mataki ne ba tare da samun hujja ba, dangane da tuhumar da take yi wa Siriya.

https://p.dw.com/p/Bvd7
Magaret Scobey, jakadiyar Amirka tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya a birnin Damascus.
Magaret Scobey, jakadiyar Amirka tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya a birnin Damascus.Hoto: AP

A lokaci daya ne, masu magana da yawun fadar White House, da kuma na ma’aikatar harkokin wajen Amirka, suka kira taron maneman labarai, don bayyana irin tsauraran matakan da gwamnatin Amirka ta dauka ko kuma ke niyyar dauka a kan Siriya, dangane da tuhumar da take yi mata, na samun hannu a harin kunan bakin waken da aka kai kan ayarin motocin tsohon Firamiyan kasar Lebanon Rafik Hariri, a birnin Beirut a ran litinin da ta wuce. Ban da shi Haririn da kansa, wannan harin ya kuma ritsa da mutane 16.

Da yake bayyana farkon matakin da gwamnatinsa ta dauka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirka, Richard Boucher, ya fada wa maneman labarai cewa:-

"Jakadiyarmu Margaret Scobey, za ta dawo Washington daga birnin Damascus, ba da wani jinkiri ba. Bisa kisan gillar da aka yi wa tsohon Firamiya Hariri, jakadiya Scobey, ta bayyana wa gwamnatin Siriya matukar bacin ranmu, game da wannan mummunan danyen aiki na ta’addanci."

Amma har ila yau dai, babu wani a da’irar gwamnatin Amirkan, wanda ke da tabbataccen hujja na jibinta mahukunta birnin Damascus da samun hannu a harin bam din da aka kai a birnin Beirut, a ran litinin da ta wuce, inda ban da asarar rayukan da aka yi, mutane fiiye da dari da 30 suka ji munanan raunuka.

A nasa bangaren, kakakin fadar White House, McClellan, ya bayyana cewa, Amirka, ta sami hadin kan gwamnatin Faransa, wajen neman kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya, ya gudanad da bincike mai zurfi kan dalilan bayan shinge, da suka janyo kai wannan harin. Ban da dai wannan batun, kakakin ya kara bayyana cewa:-

"Muna da jerin matsaloli da dama game da Siriya. Muna son dai ganin cewa, kasar ta sake halayyarta, ta kuma taka muhimmiyar rawar gani a yankin Gabas Ta Tsakiya. Har ila yau dai, muna kuma bukatar ganin cewa, gwamnatin Siriya, ta yi amfani da angizonta, wajen hana aukuwar irin wadannan hare-haren ta’addancin ma gaba daya. Bugu da kari kuma, wanzuwar dakarun Siriyan a kasar Lebanon, na kara dagula al’amura a yankin a zahiri."

Amirkan dai na ganin wanzuwar dakarun Siriyan a Lebanon, tamkar take kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1559 ne, kudurin da aka zartar a shekarar bara, wanda kuma ke da gurin ganin cewa an janye duk dakarun ketare daga kasar ta Lebanon. Ban da hakan kuma, tun da dadewa ne, Amirka ke zargin Siriya da daure wa magoya bayan Saddam Hussein gindi, da ba su mafaka, da kuma ba su damar kurdadawa cikin Iraqi daga harabarta, don gudanad da ayyukan ta’addanci.

Ko makwanni biyu ba a yi ba, da shugaba Bush na Amirka, a cikin jawabinsa na matsayin kasar, ya yi kakkausar suka ga Siriyan da cewa:-

"Siriya na bai wa `yan ta’adda, masu yunkurin yi wa duk shirye-shiryen samad da zaman lafiya a yankin kafar ungulu, damar yin amfani da harabarta da yankunan Lebanon, wajen gudanad da danyen aikinsu".

Bisa yadda al’amura suka kasance jiya a birnin Washington dai, babu wata masaniya game da lokacin da jakadiyar Amirkan za ta koma kan aikinta a birnin Damascus.