1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

310810 Irak Amerikaner

August 31, 2010

A hukumance Amurka ta kawo ƙarshen yakin da ta kwashe shekaru bakwai tana gwabzawa a Iraqi.

https://p.dw.com/p/P1F2
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: AP

A hukumance Amurka ta kawo ƙarshen yakin da ta kwashe shekaru bakwai tana gwabzawa a Iraqi. Yawancin Amurkawa na buƙatar ganin an kawo ƙarshen yaƙin baki ɗayansa. Sai dai kuma jama'a da dama na baiyana shakku dangane da makomar tsaro a ƙasar Iraqin.   

Ga dukkan wanda ke wucewa dandalin tarihi na Amirka a birnin Washington  zai lura ta kowace kusurwa da tarihin gwagwarmayar sojin ƙasar. Alal misali akwai jadawalin sunayen mutane 58,627 waɗanda suka rasu a lokacin yaƙin Vietnam da aka zayyana domin karrama su. Hakanan da wasu alamu na karrama sojojin da suka kwanta dama waɗanda suka sadaukar da rayuwar su suka kuma nuna jaruntaka a yaƙe-yaƙe daban daban da suka haɗa da yaƙin duniya na biyu.

Großbritannien Irak Soldat bei Basra Tschüß
Wani Jam'in soji a birnin Basra na ƙasar IraqiHoto: AP

Mai yiwuwa nan ba da jimawa ba a samar da wani dandalin na karrama yaƙin Iraqi wanda ya gudana daga watan Maris na shekara ta 2003 zuwa watan Augusta na shekarar 2010, ko da yake a cewar Jim daga Cincinnati yace ba shi da yaƙini akan hakan. Ya ce yadda yake kallon baki ɗayan al'amarin shine cewa janye sojojin Amirka daga Iraqi ba shi ne ƙarshen yaƙin ba.

" Ba za su taɓa ficewa ba, wannan lamari ne wanda abin takaici ya samo asali tsawon shekaru da dama ina gani ma dai zai cigaba tsawon shekaru masu yawa watakila ma har ƙarshen rayuwar mu."

Sai dai yayin da Jim wanda ɗan sa shima soja ne da kuma ya shafe shekara ɗaya a Iraqi yake baiyana shakku, shi kuwa wani soja mai suna Justin Walker na da mabanbancin ra'ayi.

" Ina gani abu ne mai kyau, nima na kasance a can Iraqi na ɗan wani lokaci, ko da yaushe al'amura sai ƙara rincabewa suke yi, muna tunanin shin wai me muke yi kuma yaushe za mu gama wannan aiki domin abin sai cigaba yake yi".

Shi kuwa Bruce Bates na da ra'ayi ne makamancin na kashi biyu bisa uku na Amirkawa waɗanda ke ganin shawarar da Obama ya yanke ta rage yawan sojojin Amirka a Iraqi a wannan lokaci ya yi daidai. " Lokaci ya yi da za mu ga ko zasu iya riƙe ragamar tsaron ƙasarsu".

Kommandoübergabe in der Grünen Zone in Bagdad
Kwamandan sojin Amirka Col. Steven Ferrari, tare da kwamandan sojin Iraqi Brigadier Emad Yaseen, a birnin BagadazaHoto: AP

Larry Hayworth mai shekaru 73 da haihuwa wanda kuma ya yi shekaru biyu a yaƙin Vietnam yana da imanin cewa za'a yi nasarar samun zaman lafiya a Iraqi duk da ƙaruwar tashe tashen hankula a ƙasar a yan makonnin nan.

" Ina fata, kuma na yi imani mun taimaka musu har izuwa matsayin da za su iya tsarawa kan su abin da suke bukata ba tare da wani daga waje ya gaya musu ga abin da za su yi ba".

Bayan tsawon shekaru bakwai ana gwabza yaƙin Iraqi, Amirkawa da dama sun ƙosa sun gajin da yaƙin. Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan ta nuna kashi biyu bisa uku na Amirkawan basa goyon bayan yaƙin, inda da dama daga cikin su ke cewa yaƙin bai tsinana komai ba, hasali ma babu wata nasara da aka cimma. Jim mahaifin ɗaya daga cikin sojojin yace Amirkawa 4,400 aka kashe a wannan yaƙi.

" Yace hasarar rai guda hasara ce mai yawa. to amma akwai mutane da dama waɗanda ke neman kashe mu saboda kawai abin da muka yi imani da shi da kuma aƙidar mu, suna nan kuma a ko ina a duniya, a saboda haka ra'ayi na shine mu yaƙe su a can inda suke maimakon a nan ƙasarmu".

Shi ma Bruce Bates na ganin sadaukarwar da Amirka ta yi ta rayuka da dukiya abu ne da ya dace. " Abin da mu ka yi kwalliya ta biya kuɗin sabulu musamman wajen kafa ginshiƙin dimokraɗiyya a wannan ɓangare na duniya da ya zama koma baya".

A ranar Talatar nan ce shugaba Obama zai yi jawabi ga rundunar sojin. Ko me Bates ke fatan ji daga Obama. " Zan so in ji yace ko da yake mun shirya barin ƙasar amma idan tarzoma ta ci gaba muna iya komawa sun san da haka".

Sai dai Annie wace saurayinta ke cikin sojojin da suka dawo gida na mai cewa " Ina tsammanin ba sai mun sake komawa ba, wannan ita ce addu'a da kuma fatan da na ke yi.

Mawallafa : Sabine,Müller / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu