Amirka ta nemi 'ya'yanta da su kaurace wa Kabul
April 11, 2016Talla
Ofishin jakadancin ya kara da cewar ya na shawarartar duk wasu Amerikawa da su kaucewar otel din tare da zama cikin shirin ko ta kwana a yayin da suke halartar gidajen otel a birnin na Kabul.
Shi dai wannan gargadin na zuwa ne bayan wasu rokoki da aka harba a yankin da ofisoshin Diplomasiya suke a ranar asabar din nan jim kadan bayan Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gudanar da wani taro da Shugabanin kasar ta Afghanistan a birnin Kabul.