1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta tashi haiƙan akan HIV/AIDS.

July 14, 2010

Gwamnatin Amirka ta gabatar da gagrumin shirin yaƙi da HIV/AIDS.

https://p.dw.com/p/OIY5
Wata mata baƙar fatan Amirka ɗauke da alamar yaƙi da cutar HIV/AIDS.Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Amirka ta gabatar da wata sabuwar dabara irinta ta farko da za ta yi amfani da ita wajen yaƙi da cutar HIV/AIDS. Sakatariyar kiwon lafiya ta Amirka, Kathleen Sibelius ta ce manufar wannan shiri ita ce rage matsayin kamuwa da cutar ta HIV/AIDS da kashi 25 daga cikin ɗari cikin shekaru biyar masu zuwa. Wannan shiri zai buƙaci ɗaukar matakan kandagarki tsakanin waɗanda ke fuskantar haɗarin kamuwa da cutar da suka haɗa da 'yan maɗigo da luwaɗi, baƙar fatan Amirka, mata da Amirkawa 'yan asalin Latin Amirka da kuma masu ɗaukar miyagun ƙwayoyi. Gwamnatin tana kuma shirin ƙara wayar da kan ɗokacin al'uma game da cutar HIV/AIDS da kuma matakan daƙile yaɗuwarta . Shekaru talatin kenan dai da duniya ta fara mai da hankali ga cutar HIV/AIDS da ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 600 a ƙasar ta Amirka. Ƙididdigar da gwamnatin Amirka ta bayar ta bayyanar da cewa a halin yanzu akwai Amirkawa miliyan ɗaya da dubu ɗari da ke ɗauke da ƙwayar wannan cuta.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu