1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aiyukan dakarun Afirka kan al-Shabab na kyau

Yusuf BalaJuly 27, 2015

A cewar Obama tallafin da Habasha ke bayarwa wajen yaki da mayakan na al-Shabab cikin dakarun kasashen Afirka ya yi baya.

https://p.dw.com/p/1G5PL
Äthiopien Barack Obama Hailemariam Desalegn PK
Shugaba Obama da Hailemariam Desalegn na HabashaHoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana cewa yadda dakarun sojan kawancen Afirka na AU da dakarun sojan Somaliya ke kara matsa lamba kan mayakan al-Shabab abin a yaba ne, sai dai ya kara cewa dole ne a sake dagewa kan wadannan mayaka masu tada kayar baya.

Da yake jawabi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha shugaba Obama ya ce mayakan na al-Shabab babu abin da suka sanya a gabansu sai halakar da jama'a da lalata gine-gine.

A cewar shugaba Obama kasar ta Habasha na da babbar barazana da ke a gabanta, abin da ya sanya dole su tashi tsaye dan fiskantar wannan kalubale.

"Hadin kanmu a bangaren tsaro shi ne mu tunkari masu tsatstsauran ra'ayi . Kasar Habasha na fiskantar babban kalubale sannan tallafin da take bayarwa wajen yaki da mayakan na al-Shabab cikin dakarun kasashen Afrika ya yi baya, amma kamar yadda Firaministan kasar ya gani a ranar Lahadi a harin birnin Mogadishu babu abinda mayakan suka sa gaba sai ganin suna kwararar da jini da lalata wurare abinda ya sa muke da aiki ja a gabanmu."