1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi barazanar aiwatad da wani shirinta na sirri kann Sudan idan ba ta amince da girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur ba.

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bub4

Wani babban jami’in gwamnatin Amirka ya yi barazanar cewa, mahukuntan birnin Washington, za su fara aiwatad da wani matakin sirrin da suka shirya kan Sudan, idan ƙasar ba ta amince da girke dakarun kare zaman lafiyar Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur kafin ran 1 ga watan Janairu mai zuwa ba.

Rikicin da ake yi a yankin tun shekara ta 2003 dai, ya janyo asarar rayukan mutane fiye da dubu ɗari 2. Jami’in Andrew Natsios, ya ce a kwanakin bayan dai, an yi ta ƙara samun hare-haren da ake kai wa fararen hula a yankin. Sai dai bai ba da ƙarin haske game da matakin da gwamnatin Amirkan ke barazanar ɗauka ba. A ran 1 ga watan Janairun shekarar baɗi ne dai wa’adin girke dakarun kare zaman lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU zai cika. Ita kuma Sudan ɗin na daddage wa duk wani yunƙuri ne na girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasarta, saboda abin da take gani kamar wani sabon mulkin mallaka ne ake son yi mata,.