1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta bunkasa makamashi a Afirka

Abdullahi Tanko Bala/A'RaheemSeptember 21, 2016

Shugaban Amirka Barack Obama ya kaddamar da yunkurin bunkasa makamashi a Afirka tare da baiyana kudirin hukumomi da yan kasuwar Amirka na samar da tsabar kudi Dala biliyan daya domin aiwatar da shirin.

https://p.dw.com/p/1K6Ff
New York UN Generalversammlung Rede Obama
Barack ObamaHoto: picture-alliance/dpa/Li Muzi

A wani taro tsakanin yan kasuwar Amirka da na Afirka da ya gudana a daura da taron kolin Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a wannan makon aka cimma kudirin aiwatar da shirin wnda aka yiwa lakabi da " Power Africa" na samar da ingantaccen makamashi ga Afirka a cewar shugabanr hukumar taimakon raya kasashe ta Amurka USAID Gayle Smith na da nufin samar da wutar lantarki mai karfi ga Afirka.

Obama ya fara kaddamar da shirin ne a shekarar 2013 da alkawarin zuba jarin dala biliyan bakwai domin samar da wutar lantarki mai karfin megawatts dubu goma da ake fatan mutane miliyan ashirin za su ci moriyarsa tare da tabbatar da dorewar wutar lantarkin ko ina a Afirka kudu da hamadar sahara. Shirin har ila yau yana fatan jawo yan kasuwa masu zaman kansu su zuba jari a harkar makamashi a yankin inda tarnaki na hukumomin lura da harkar makamashin da kuma rashin tsarin takaita hasara suka sanya masu juba jari daga kasashen yamma suka kaurace. Shugabar hukumar taimakon raya kasashe ta Amirka Gayle Smith ta ce shirin wanda ya tanadi samar da kudade da rage hasara ta hanyar Inshora da sabbin dabarun makamashi za'a aiwatar da shi ne a kasashen Kenya da Najeriya da Senegal da Saliyo da Afirka ta kudu da kuma Tanzania.

USA Flüchtlingsgipfel Barack Obama
Shugaban kasar Amirka, Barack Obama.Hoto: Reuters/B. McDermid

Kawo yanzu dai shirin bunkasa makamashin a Afirka ya samar da Dala biliyan 52 inda daga cikin wannan adadi Dala biliyan 40 suka fito daga kamfanoni masu zaman kan su a cewar hukumar bada taimakon raya kasashe masu tasowa USAID wadda ita ce ke lura da aiwatar da shirin a yankin na Afirka. Sai dai kuma ta ce yayin da ake sukar tafiyar hawainiya na fara aiwatar da shirin, a waje guda ta ce a yanzu shirin ya fara kankama. Smith ta ce zartar da dokar da majalisun wakilai dana dattijan Amirka suka yi kan kudirin bunkasa wutar lantarki a Afirka wata alama ce da ke nuna wannan abu ne da Amirka za ta ci gaba da shi ko da bayan wucewar gwamnatin Obama. To sai dai abin tambaya shi ne me yasa Amirka da dauki wannan kuma me hakan ke nufi ga nahiyar Afirka? Shikwati daraktan kungiyar nazarin tattalin arziki a tsakanin yankunan Afirka ya ce:

" Da farko Afirka na bukata samun makamashi domin aiwatar da shirin bunkasa masana'antunta, saboda haka Amirka ta na wannan ne domin aiwatar da bukatar da dama ake da ita a kasa ta samar da makamsashi a Afirka."

James Shikwati Direktor bei IREN in Nairobi
Daraktan kungiyar nazarin tattalin arziki a nahiyar Afirka James Shikwati.Hoto: DW/T. Mösch

Wani yanki na wannan kudi da zai zo a matsayin bashi kuma a galibin lokuta kasashe kan kasa biyan bashin saboda wasu dalilai walau na gudanarwa ko kuma na almundahana da sama da fadi da dukiyar hukuma.