1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290310 Todesstrafe Amnesty

March 30, 2010

Hukumar kare haƙƙoƙin bani Adama ta ƙasa da ƙasa Amnesty International ta bayyana rahoto game da hukuncin kisa cikin duniya a shekara ta 2009

https://p.dw.com/p/MhrR
Amnesty international ta bayyana rahoton hukuncin kisa a shekara 2009

 Hukumar kare haƙƙoƙin bani Adama ta ƙasa da ƙasa wato Amnesty International ta bayana rahoton shekara da ta gabata game da hukunci kisa a duniya.

A cewar rahoton na Amnesty International  a shekara 2009 mutane 714 aka yankewa hukuncin kisa, kuma aka kashe a cikin ƙasashe 18.Sannan yawan mutanen da aka yankewa hukuncin kisa wanda ba a riga aka zartas da hukuncin ba sun kai 2000  a cikin ƙasashe 56 na duniya. Sakatare Janar ta hukumar Amnesty International reshen ƙasar Jamus  Monika Lüke tayi suka da kakkausar halshe game da ƙasar Sin wadda tayi ƙaurin suna ta fannin hukunci kisa, tace

babu shakka ƙasar Sin itace ke sahun gaba game da hukuncin kisa,Duk da cewar babu alƙaluma cikkaku agame da yawan mutane da ka kashe ta wannan hanya amma mun yi imanin cewar dubunnai ne.

Monika Lüke ta ce akwai hazo ƙwarai game da yawan rayukan da suka salwanta a bara a ƙasar Sin ta hanyar hukuncin kisa.

Bayan ƙasar Sin, daga  ƙasashen da Amnesty ta tantance yawan mutanen da aka kashe bara ƙasar Iran ke kan gaba, tare da kisan mutane aƙalla 390 sai Irak ke bi mata da mutane fiye da 120, sannan Saudi Arabiya da Amurika.A hanyar Afrika ƙasashe da suka zartas da hukunci kisa a shekara bara sun haɗa da Sudan, Masar, Libiya da Botswana.

A ƙasashen  Iran, Irak da Sudan,akasari hukuncin kisan da aka yanke, ya shafi ´yan siyasa na ɓangaren jam´iyun adawa inji Monika Lücke:

"A shekara ta 2009, a ƙasar Iran mun tantance mutane 388 da aka kashe ta hanyar hukunci kissa, dukan su ´yan adawa, bayan zaɓen   Mahamud Ahmedinedjad. Wannan mutane sun haɗa da yara ´yan ƙasa ga shekaru 18, abinda kwata-kwata ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa."

A ɗaya wajen, Sakatare Janar ta hukumar Amesty International reshen Jamus ta bayyana Amurika  a matsayin ƙasar da hukuncin kisa ke ƙara yaɗuwa a cikin jihohi.Tace a shekara 2008 mutane 30 ne aka kashe  a yayin da bara yawan su ya kai fiye da 50.

Saidai a ɗaya wajen, ta yaba ci gaba da aka samu ta fannin ƙarin ƙasashen da suka yi watsi da hukuncin kisa, wanda a halin yanzu yawan su ya kai 139.

A lokacin da Amnesty ta fara gwagwarmayar yaƙi da hukuncin kisa a shekara 1977 ƙasashe 15 kacal suka haramta hukuncin kisa.Hatta a shekara bara ƙasashe biyu na Afrika, Togo da Burundi sun haramta hukunci kisa.Haka zalika,  a ƙasashen Turai ma  shekara 2009, babu mahalukin da ya rasa rai sanadiyar hukuncin kisa.

Don ƙara ƙarfafa wannan cigaba Monika Lücke tace Amnesty ba zata ƙasa a gwiwa ba:

"Zamu cigaba da matsa ƙaimi ga gwamnatocin ƙasashen dake da hukuncin kisa, sannan zamu aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da wannan hukunci.A duk inda muka sami labarin an yanke wannan hukunci kamar yadda ta wakana kwananan a Texas ƙasar Amurika zamu rubuta wasiƙu domin mu ƙalubalanci al´amarin".

Don cimma burin kauda wannnan hukunci daga duniya Monika Lücke tayi kira ga gwamnatin Jamus ta bada babbar gudummuwa mussaman wajen ƙasashe kamar su Amurika da Japan.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita : Abdullahi Tanko Bala