1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty International ta gabatad da rahotonta

YAHAYA AHMEDMay 23, 2006

Ƙungiyar fafutukar kare hakkin ɗan Adam nan Amnesty IInternational, ta gabatad da rahotonta na shekara-shekara, inda ta yi kakkausar suka ga Amirka, da kasancewa jagora a ƙasashen yamma wajen take hakkin ɗan Adam, musamman a sansanoninta da ke Guantanamo Bay da wasu wurare a nahiyar Turai, sa'annan kuma a Iraqi da Afghanistan.

https://p.dw.com/p/BvTa

A kusan ko’ina a duniya dai, dalilan da ke janyo take hakkin ɗan Adam kusan ɗaya ne. Ko dai ana yin haka ne don nuna iko a fagen siyasa, ko kuma saboda dalilan da ke da jiɓinta da tattalin arziki. Gwagwarmaya kan madafan iko, ko tabbatad da angizon wasu a kan samun albarkatun ƙasa na cikin muhimman ummal aba’isin take hakkin ɗan Adam. A galibi, ana ci wa jama’a zarafinsu da take musu hakkokinsu ne, saboda a hana su buɗe baki su yi magana a kan rashin nuna adalcin da suke gani ana yi musu. Masu ƙoƙarin magana da yawunsu kuma, kamar dai kafofin yaɗa labarai da ’yan jaridu, su ma ba su tsira ba.

Burin da duk masu take wa jama’a, musamman ma dai tsiraru hakkinsu, shi ne yunƙurin yi musu danniya da kuma mamaye matsugunansu da albarkatun ƙasar da ke cikinsu. A galibi, suna hakan ne kuma saboda suna riƙe da madafn iko. Kuma sai su yi amfani da wannan damar, wajen ƙirƙiro wani salo, wai na tabbatad da tsaro, da samad da zaman lafiya da kuma kare ’yancin ƙasar da suke ikon. A ƙasashen Sin da Rasha a lal misali, waɗanda ke cikin masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, mahukuntansu na hujjanta take hakkin ɗan Adam da suke yi a yankin Checheniya da jihar Xinjiang ne da cewa, duk matakan da suke ɗauka, na kare haɗin kan ƙasashensu ne daga yunƙurin da ’yan aware ko kuma ’yan ta’adda ke yi na rarraba ƙasar.

Nahiyar Afirka ma, ba a bar ta baya ba a wannan huskar. Akwai yaƙe-yaƙen ƙabilanci da kashe-kashen gilla da suka auku a yankuna da dama na nahiyar. Haka kuma ake samu a wasu yankunan na Asiya da Latinamirka da Gabas Ta Tsakiya.

Amma rahoton na Amnesty International, bai tsaya kawai a ƙasashe masu tasowan ba. Ba ya kuma zargin wasu yankuna ko ƙabilu na wannan nau’in na ƙasashe masu tasowan. Yana bayyana irin take hakkin ɗan Adam da aka yi ne a ko’ina, daga ƙasashe masu mulkin kama karya kamarsu Korea Ta Arewa, ko kuma irin take hakkin bil’Adama da ake yi a na wani salo daban, a ƙasashe kamarsu Zimbabwe ko Saudiyya. Kazalika kuma, rahoton bai kare ƙasashe dimukraɗiyya na yamma daga suka ba. Ya yi Allah wadai da irin halin da fursunoni ke ciki a gidajen yari a wasu ƙasashen na yamma, kamarsu Italiya da Girka. Ta haka ne kuma, ya yi tofin allah tsine ga take hakkin ɗan Adam da ake yi a Isra’ila da kuma wanda rukunan ƙungiyoyin Falasɗinawa ke aikatawa.

A nan cikin gida Jamus kuma, rahoton ya zargi gwamnatin tarayya da rashin nuna sassauci ga maneman mafaka, waɗanda aka tabbatar cewa, idan an mai da su ƙasashensu, za su huskanci matsaloli iri-iri, daga ɗauri da shan azaba a kurkuku, har zuwa yanke musu hukuncin kisa.

Amma ƙasar yamma da ta fi shan kakkausar suka daga ƙungiyar ta Amnesty International, saboda take hakkin ɗan Adam mafi munin da take ta aikatawa, ita ce Amirka. Ƙungiyar ta ce Amirka tana mummunan take hakkin ɗan Adam a sansanin Guantanamo Bay, da Iraqi da Afghanistan da ma wasu gidajen yarin sirri na ƙungiyar leƙen asirin CIA da ke nan Turai. Ta dai yi suka ne musamman ga gallaza wa fursunoni da jami’anta ke yi, wai saboda tsaron ƙasa ko kuma yaƙi da ta’addanci.

A taƙaice dai, ƙungiyar ta yi kira ga duk ƙasashe masu bin tafarkin dimukraɗiyya da kada su manta da harsashen ginin da wannan tafarkin ke bisa kai, wato na cewa, take hakkin ɗan Adam ba zai taɓa janyo zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. A daura da haka ma, sai taɓarbarewar halin tsaro zai iya janyowa.