1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta binci yakin Mosul

Abdul-raheem Hassan
July 11, 2017

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty international, ta wallafa rahoton dake nuna karfin makamai da 'yan tawaye da sojojin gwamnati suka yaki juna, ya wuce gona da iri da a yanzu ya shiga jerin laifukan yaki.

https://p.dw.com/p/2gLWd
Irak Kampf um Mossul
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye

Rahoton na Amnnesty na cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar Mayu, an kai hare hare 45 wanda yayi sanadiyar mutuwar fararen hula 426. A watan Oktoban shekara ta 2016 ne dakarun gwamnatin Iraki dake samun goyoyn bayan sojojin Amirka, suka kaddamar da yaki na musamman a kan mayakan IS da nufin maida birnin Mosul a hannun gwamnati.

Binciken kungiyar ya gano yadda aka gallazawa fararen hula da dama, wanda yayi sanadiyar darurwan mutane kaurace wa birnin Mosul. kungiyar ya bukaci hukunta wadan da aka samu da hannu a aikata laifukan da suka zarta misali a kan wadanda basuji ba ba su gani ba.

Wannan dai na zuwane bayan da dakarun gwamnatin Iraki suka kaddamar da hari kan wasu gungun mayakan IS dake samun mafaka a kudancin birnin Mosul, somamen dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnati ta ayyana nasarar kakkabe kungiyar IS a birnin.