1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta soki kasashen duniya kan Siriya

Mahmud Yaya Azare/ASSeptember 16, 2016

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta nuna damuwa kan mawuyacin halin da dubban masu neman mafaka 'yan kasar Sirya ke ciki a kan iyakar kasar Jordan.

https://p.dw.com/p/1K3u1
Amnesty International
Hoto: picture-alliance/dpa

Amnesty International ta ce watsi da aka yi da 'yan Siriya din da ke neman mafaka ya sanyasu kasancewa cikin hadari na rasa rayukansu inda ta kafa da wasu hotunan na tauraron dan Adam da ta nuna. Hotunan dai sun nuna wasu daga cikin wadannan mutane a mace a sansanin Rukhbah da ke kan iyakar kasar Siriya da Jordon bayan da suka samu kansu cikin halin gaba kura baya siyaki domin kuwa rikicin kasarsu ya hana su zama cikinta yayin da ita kuma kasar Jordan ta hanasu shiga.

Wani mutum da ke cikin dinbin 'yan gudun hijira ya shaidawa DW cewar ''mun zo nan ne don gujewa lugudan wutar da ake mana. Ga mu yanzu zube a hamadar Allah. Mutane da dama sun mutu don yunwa ko jinya. Wasu mutane sun zo sun dan kawo mana kayayyakin agaji." Sansanin na Rukhbah da kungiyar ta Amnesty International ta ce 'yan gudun hijira fiye da dubu 75 na makale cikinsa ba shi da wadataccen ruwan sha da abinci kuma cututtuka na cigaba da yaduwa a cikinsa dalilin da ya sanya kungiyar likitocin Nagari Na Kowa wato Doctors Without Borders kiransa da suna "sansanin mutuwa" saboda zai yi matukar wuya a iya rayuwa cikinsa kasantuwarsa cikin kungurumin hamada yadda baka jin komai cikinsa sai rugugin guguwar da ke watsa zazzafan rairayi.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce mutane hudu cikin biyar dake sansanin mata ne da yara kananan da ke saurin galabaita. A watan Mayun da ya gabata dai mahukuntan na Jordan da suka dage kan sai 'yan gudun hijirar sun koma inda suka fito sun bari an shigar da 'yan kayayyakin agaji sansanin amma daga baya suko komo suka rufe shi bayan da kungiyar IS ta kai wani harin kunar bakin wake da ya kashe sojojin kasar shida da ke kusa da sansanin.

Syrien Jordanien Grenze Flüchtlinge warten
Dubban 'yan Siriya ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira da ke kan iyakar kasar da JordanHoto: picture-alliance/AP Photo/R. Adayleh