1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnisty ta yi kira ga hukumomin soja na Birmania da su yi belin Aung san Suu Kyi

June 19, 2006
https://p.dw.com/p/ButK

Hukumar kare haƙƙoƙin bani Adama ta dunia, Amnisty International ta yi ,kira ga da hukumomin Birmania, da su yi belin Aung San Suu kyi, jagorar yan adawar wannan ƙasa.

Wannan Kira, ya zo a daidai lokacin da, Suu Kyi, ke cika shekaru 61 a dunia.

A tsawan shekaru 17 da su ka gabata, Aung San Suu Kyi, ta share zaman kurkuku na shekaru 10.

Jam´iyar da ta ke jagoranta, wato LND, ta lashe zaɓe a shekara ta 1990, amma sojojin da ke karagar mulki tun1962, su ka yi mata murɗiya.

A watan Mai, da ya gabata, hukumomin Rangoun babban birnin ƙasar su ka tsawaita ɗaurin talala, ga jagorarar yan adawar, duk kuwa da kiran da ƙasashen dunia ke ci gaba da yi masu na yin belin ta.

Alƙalluman Majalisar Ɗinkin Dunia, sun tabbatar da cewa, bayan Aung San Suu Kyi, akwai a yanzu haka, wasu pirsinonin siyasa dubu 1, da ɗari 1,a ƙasar Birmania.

A ranar yau litinin, an tsarta gudanar da zanga-zanga, a ƙasashe da dama na dunia, domin nuna goyan baya, ga Aung san Suu kyi.