1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnystie Intrenational ta zargi Sin da Russia da tura makamai a Sudan

May 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuLm

Ƙungiyar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa, wato Amnisty International, ta zargi ƙasashen Sin da Russie, da karya takunkumin MDD, na haramta sayar da makamai ga Sudan.

Wani rahoton da ƙungiyar ta hiddo, ta bayyana takaici a game da yadda ƙasashen 2 ke ci gaba da jibge makamai a ƙasar Sudan, wanda a cewar wannan rahoto, ake anfani da su wajen kai hare hare a yankin Darfur da ma kasar Tchad da ke maƙwabtaka da Sudan.

Ba da wata wata ba, Sin da Russia sun maida martani a game da wannan zargi, da su ka ce bashi da tushe bare makama.

Kazalika hukumomin Khartum, sun sa ƙafa sun shure rahoton na Amnisty International, wanda a cewar su, babu ƙanshi gaskiya a cikin sa.